A jiya 16 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani sharhi, wanda ke da lakabin "tabbas ne kungiyar Dalai Lama za ta ci tura a yunkurinta na lalata kwanciyar hankali a Tibet.
Sharhin ya ce, kwanan baya, wasu tsirarrun mutane sun yi ta barna a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, a kan yunkurin lalata tsarin zaman al'umma da kawo hasarori ga rayuka da dukiyoyi na jama'a. Sassan da abin ya shafa na jihar Tibet sun dauki matakai kamar yadda ya kamata, yanzu an kwantar da kurar tarzomar.
Sharhin ya ce, a ran 10 ga wata da yamma, duk da dokokin kasar Sin da ka'idojin gidan ibada, wasu mabiya addinin Buddah kimanin 300 na wurin sun yi yunkurin shiga birnin Lhasa don neman tayar da tarzoma. Tun daga ran 11 har zuwa 13 ga wata, wasu mabiya addinin Buddah sun ci gaba da taruwa, sun yi ta jefa duwatsu ga masu kiyaye tsaro tare da zuba musu lemon tsami da tafasasshen ruwa, har ma sakamakon hakan, 'yan sanda da jami'ai gomai sun ji raunuka. A ran 14 ga watan Maris kuma, wasu 'yan aware sun fara taruwa a titin Bakuo na birnin Lhasa, inda suka yi ta kiran ballewa da kuma duke-duken jama'a da farfasa abubuwa da washe kayayyaki da kuma kone gine-gine da motoci. Bayan haka, sun kuma kai hare-hare kan ofishin 'yan sanda da hukumomi tare da washe bankuna da kantuna da gidajen mai da kuma kasuwanni. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, gaba daya 'yan tawaye suka kone gine-gine 22, ciki har da makarantu 3, tare kuma da wasu motocin 'yan sanda da na jama'a gomai. Sakamakon danyun ayyukansu kuma, wasu jama'a marasa laifi su 10 sun mutu, a yayin da 'yan sanda da sojoji 12 suka ji raunuka masu tsanani, har ma biyu daga cikinsu suna bakin mutuwa.
Sharhin ya ce, akwai kwararan hujjojin da suka shaida cewa, kungiyar Dalai Lama da ke waje ita ce ta yi makarkashiyar tarzomar tare da ba da jagoranci a kanta. Sharhin ya kara da cewa, Tibet wani yanki na kasar Sin ne wanda ba za a iya raba shi ba, tun tuni wannan ya zama ra'ayi daya na gamayyar kasa da kasa. Kungiyar Dalai Lama ta bakanta wa jama'a rai a yunkurinta na lalata kwanciyar hankali da zaman lafiya a Tibet, kuma tabbas ne za ta ci tura.(Lubabatu)
|