Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-15 21:33:42    
An shirya taron farko na zaunannen kwamiti na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Daga ran 14 zuwa 15 ga wata a birnin Beijing, an shirya taron farko na zaunannen kwamiti na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin.

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mr Jia Qinglin ya bayyana a gun taron cewa, sabon zaunannen kwamiti na majalisar zai sauke nauyin da ke bisa wuyansa cikin yakini, da kuma gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Mr Jia ya ci gaba da cewa, kamata ya yi a yi amfani da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da kyau, wadda ta kasance wata kungiyar siyasa ce da ke da tsarin dimukuradiyya na musamman, domin sa kaimi ga raya yunkurin siyasa na dimukuradiyya na gurguzu, da li,a kara hada kai a tsakanin Jam'iyyar kwaminis ta Sin, da rukunonin jam'iyyun dimukuradiyya, da mutanen da ba su shiga cikin ko wace jam'iyya, da kuma inganta tsarin majalisar, domin kara karfafa kwarewarta wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata.(Danladi)