Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-15 20:29:00    
(Sabunta) Kasar Sin ta zabi sabbin shugabannin kasar

cri

Yau 15 ga wata, 'yan majalisar wakilai kusan 3000 na kasar Sin, sun zabi sabbin shugabannin kasar bayan da suka jefa kuri'u ba tare da sanya suna ba. Mr. Hu Jintao ya cigaba da zama shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar.

An shirya zaben ne a gun cikakken zaman taro da aka shirya a wannan rana game da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. A gun taron, Mr. Wu Bangguo ya zama shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na karo na 11, Mr. Xi Jinping kuma ya zama mataimakin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Bayan haka kuma, taron ya amince da shirin yin gyare-gyaren hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar Sin. Bisa shirin, za a daidaita tsofaffin hukumomi guda 15, kasar Sin za ta kafa ma'aikatar masana'antu da aikin sadarwa, da ma'aikatar sufuri da zirga-zirga, da ma'aikatar albarkatun kwadago da jin dadin jama'a, da ma'aikatar kiyaye muhalli da kuma ma'aikatar gidaje da raya birane da kauyuka.

Hu Jintao

A wannan rana kuma, shugabannin jam'iyyu da kasashe daga kasashen Korea ta arewa, da Vietnam, da Japan, da kuma Hungary, sun aiko da talgiram, don taya murna ga sabbin shugabannin da aka zaba a gun taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 11 (Bilkisu)