Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-15 19:23:48    
Takaitaccen tarihin sabbin shugabannin kasar Sin

cri

Aminai 'yan Afrika, bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar an ce, a gun cikakken zama na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka gudanar yau Asabar a nan birnin Beijing, Mr. Hu Jintao ya sake cin zaben shugaban Jamhuriyar jama'ar Sin kuma shugaban kwamitin soji na tsakiya na kasar. Jim kadan bayan zaben, kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu iznin da aka danka masa na sanar da takaitaccen tarihi na shugaba Hu Jintao.

Mr. Hu Jintao, dan kabilar Han ne, wanda aka haife shi a shekarar 1942. An shigar da shi cikin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a shekarar 1964. Ban da wannan kuma ya samu digirin ilmi na injiniya daga Jami'ar Qinghua; A shekarar 1960, Mr. Hu ya yi aiki a ma'aikatar kula da harkokin tsare ruwa da na samar da wutar lantarki ta kasar bayan ya sauke karatu a Jami'ar; Daga baya dai, ya taba zama shugaban hadaddiyar kungiyar samari ta duk kasar da kuma sakatare na farko na satariyar kungiyar samari ta kwaminis din duk kasar; Sa'annan ya taba zama sakataren kwamitin lardin Guizhou na JKS da kuma sakataren kwamitin jam'iyya na jihar Tibet mai cin gashin kanta. Kazalika, a tsakanin shekarar 1992 zuwa 2002, ya zama wakilin din-din-din na kwamitin tsakiya na JKS, kuma sakataren sakatariyar kwamitin tsakiya na jam'iyyar bugu da kari mataimakin shugaban kasar Sin da mataimakin shugaban kwamitin soji na tsakiya na kasar; Daga shekarar 2002 ne Mr. Hu Jintao ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma mataimakin shugaban kasar bugu da kari mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na kasar; Tun daga shekarar 2003 ne ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban jamhuriyar Jama'ar Sin.Dadin dadawa, tun daga shekarar 2005 har zuwa yanzu, ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban Jamhuriyar jama'ar Sin bugu da kari shugaban kwamitin soji na tsakiya na kasar.

Jama'a masu sauraro, yanzu dai za mu kawo muku takaitaccen tarihi na shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo. Mr. Wu dan kabilar Han ne dake da shekaru 67 da haihuwa. An shigar da shi cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin a watan Afrilu na shekarar 1964. ya samu digirin ilmi na injiniya daga Jami'ar Qinghua. Ya taba yin aiki da wata ma'aikata a Shanghai bayan ya sauke karatu daga Jami'ar. Daga shekarar 1991 zuwa 2002, ya taba zama sakataren kwamitin birnin Shanghai na JKS, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar, sakataren sakatariyar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kuma mataimakin firaministan kasar; Ban da wannan kuma, tun daga shekarar 2002, Mr. Wu ya ci zaben zama wakilin din-din-din na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin; Kazalika, ya ci zaben zama shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a shekarar 2003; Bayan wa'adin aikinsa ya cika, sai ya sake cin zaben zama shugaban majalisar da aka gudanar a yau Asabar.

Aminai 'yan Afrika, yanzu bari mu karanta muku wani takaitaccen tarihi na mataimakin shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping. Mr.Xi, dan kabilar Han ne mai shekaru 55 da haihuwa. An shigar da shi cikin JKS a shekarar 1974. Ya samu digiri ilmi na dokta a fannin shari'a a Jami'a. Tuni ya taba yin aikin gona a wani kauye a lardin Shanxi. Daga baya dai, ya samu shiga jami'ar Qinghua domin koyon ilimin sarrafe-sarrafen man fetur. Tun daga shekarar 1982, ya yi aiki a lardin Hebei da lardin Fujian da kuma lardin Zhejiang har da birnin Shanghai, inda ya kama mukamin shugaban lardin Fujiang, da sakataren kwamitin lardin Zhejiang na Jam'iyyaar Kwaminis ta Sin da kuma sakataren kwamitin birnin Shanghai na JKS da dai sauran manyan mukamai. Tun shekarar da muke ciki ne Mr. Xi Jinping ya zama wakilin din-din-din na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma sakataren sakatariyar kwamitin tsakiya na jam'iyyar. ( Sani Wang)