Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 16:02:39    
Bayani kan dan sanda mai kiyaye zaman lafiya kuma dan kabilar Tibet na kasar Sin

cri

Aminai 'yan Afrika, bayan da wani dan sanda kuma dan kabilar Tibet mai suna Ciren ya samu labarin cewa an rigaya an bayyana sunansa a matsayin wani dan takarar daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics, sai ya kara yin horon gudu a kowane mako. Yana mai cewa: "Lallai bai dace ba in gajiya ta kama ni har na ja numfashi yayin da nake yin gudu na gajeren zango rike da wutar yula mai tsarki ta gasar wasannin Olympics kan titin wannan birni na Lhasa bisa babban tudu inda yake da karancin iskar Oxygen, domin kuwa a wancan lokaci dai, fuskar Sinawa ce nake bayyanawa a madadin kasar Sin".

Mr. Ciren ya furta cewa, idan ya samu alfarmar zama mai daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, to da a karo na biyu ne zai kammala muhimmiyar dawainiya a madadin kasar Sin. Tuni a watan Oktoba na shekarar 2004, rundunar 'yan sanda masu kwantar da tarzoma ta farko ta kasar Sin ta tafi kasar Haiti domin wanzar da zaman lafiya a kasar din. Mr. Ciren mai shekaru 30 da haihuwa ya yi farin ciki da samun shiga wannan runduna daga hukumar kula da harkokin shige da fice ta sashen tsaro na jihar Tibet mai cin gashin kanta ,wato ke nan ya kasance wani dan sanda na farko na cikin kasar da ya shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya tsakanin kasa da kasa. Mr. Ciren ya ce, wannan dai karo na farko ne da na yi aikin wanzar da zaman lafiya a madadin kasar Sin. " Mun kammala dawainiyoyi iri daban-daban da kyau na wanzar da zama lafiya a kasar Haiti. 'Yan sanda na kasar sun buga babban take a gare mu. A lokacin kiyaye zaman lafiya a kasar Haiti, mun yi fice wajen kammala dukkan dawainiyoyi. 'Yan sanda na musamman na kasar Haiti sun jinjina mana akan cewa ' Mun kware sosai a aikinmu'."

Tun da farko saukarmu a kasar Haiti, mun dai yi zama cikin muhalli maras kyau, ba mu da wurin kwana da kuma abubuwan masarufi. Hakan ya tilasta mana dora aikin kafa wani sansani a gaban komai. 'Yan sanda masu kwantar da tarzoma na kasar Sin sun sami hadari ba sau daya ba sau biyu ba yayin da suke jigilar kayayyakin gine-gine a kan hanya, inda wasu 'yan takife sukan yi fashi da makamai da kuma harbe-harbe. Mr. Ciren sau da yawa ne ya fid da jin tsoro wajen jigilar kayayyaki, ya kuma yi sauran ayyuka da dama, wadanda bai taba yinsu a cikin gidan kasar mahaifa ba.

Ba kamar yadda 'yan sanda masu kiyaye zaman lafiya suke yi ba, 'yan sanda masu kwantar da tarzoma suna kuma daukar dawainiyar gwabza fada. Lallai ba a manta ba, a ranar 4 ga watan janairu da daddare na shekarar 2005, Mr. Ciren da wasu takwarorin aikinsa sun yi sintiri kan titi, nan take wani mutum na wurin ya zo gabansu yana mai cewa dan uwansa ya ji rauni mai tsanani a kafarsa bayan da 'yan fashi suka harbe shi. Da Mr. Ciren ya ji haka, sai nan da nan ya tafi inda lamarin ya auku don kai mai jin raunin asibiti, wanda a karshe ya tsallake rijiya da baya.

Aikin kiyaye zaman lafiya na tsawon watanni shida a kasar Haiti ya zama wani abun da Mr. Ciren ba zai manta da shi ba a duk tsawon rayuwarsa domin kuwa a wancan lokaci, da shi da abokansa sun sha fama da yanayi mai zafi da kuma cizon sauro da kwari da dai sauran cututtuka.

Ayyukan da 'yan sanda masu kwantar da tarzoma na kasar Sin suka yi sun samu karbuwa sosai daga gwamnatin kasar Haiti, da gamayyar kasa da kasa da kuma gwamnatin kasar Sin. Sun kuma samu lambar yabo daga kungiyar musamman ta MDD a kasar Haitu.Mr. Ciren shi ma ya samu lambar yabo ta musamman bisa fitaccen aikin da ya yi a kasar Haiti.

Mr. Ciren ya ci gaba da yin aiki a matsayin wani dan sanda na jama'a bayan ya koma bakin aikinsa. Yana mai sha'awar wasan kwallon tebur. Ya fada wa wakilinmu cewa: " Karfin zuciya da 'yan wasan kwallon tebur na kasar Sin sukan nuna a gun gasa ya cancanci na yi koyi da shi a duk tsawon lokacin da nake aiki domin jama'a. Mr. Ciren bai taba yin tsammanin samun damar yin cudanya kai tsaye tare da wasannin Olympics kafin ya zama mai daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijijg ba. Ya yi farin ciki matuka da fadin cewa: " A matsayina na wani wakilin 'yan sanda na jihar Tibet mai cin gashin kanta, na kuduri aniyar kara yin azama don cimma kyakkyawan buri irina na wasannin Olympics, da yayata hasashen Olympics na zaman lafiya da zumunci da kuma na zaman jituwa ga dukkan fadin duniya ta hanyar mika wutar yula a wannan shekara".(Sani Wang)