Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 15:50:45    
Labarin wata wakiliyar CPPCC

cri

Kamar yadda kuka sami labarin cewa, a yanzu haka dai ana gudanar da manyan tarurruka biyu a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Wadannan tarurruka biyu kuma sun kasance wani al'amari mai matukar muhimmanci a fagen siyasa na kasar Sin, kuma bayan da aka bude su a farkon watan nan da muke ciki, sai bi da bi ne masu sauraronmu suka turo mana tambayoyi, inda suka nemi karin bayani a game da tarurrukan, kuma idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata a wannan filinmu na "amsoshin wasikunku", mun kawo muku wani bayani dangane da taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, a wannan mako kuma, bari mu bayyana muku taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ko CPPCC a takaice. Domin ku sami fahimtar rawar da taron ke takawa a kasar Sin sosai, wakilinmu ya yi hira da wata wakiliyar majalisar. To, yanzu sai ku gyara zama, ku saurari labarin wannan wakiliyar.

Malama Wei Wei wadda ke da shekaru 60 da haihuwa ta zo ne daga lardin Shanxi da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma a wannan shekara, a karo na uku ne, ta zama wakiliyar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Tun daga shekarar 1998, a watan Maris na kowace shekara, Madam Wei Wei ta kan zo nan birnin Beijing, domin halartar taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa, wato CPPCC, ta yadda za ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta na sa hannu cikin harkokin siyasa a matsayin wakiliyar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa.

Madam Wei Wei ta ce, "idan aka kwatanta zamana a taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa da aka yi a shekaru 10 da suka wuce da na yanzu, yanzu ba na cike da annashuwa sosai, kuma a maimakon hakan dai, abin da na ji shi ne babban nauyin da ke bisa wuyata."

Ba da shawarwari ga gwamnatin kasar Sin ta hanyar gabatar da shirye-shirye wata muhimmiyar hanya ce da wakilan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ke bi wajen sauke nauyin da ke bisa wuyansu na sa hannu cikin harkokin siyasa. A cikin shekaru 10 da suka wuce, a kalla dai madam Wei Wei ta kan gabatar da shirye-shirye guda biyar a kowace shekara. A wannan shekara kuma, gaba daya ta kawo shirye shirye 10, wadanda ke shafar kafa tsari bai daya na biyan kudin jinya da kiyaye muhalli a yayin da ake aiwatar da shirin jigilar ruwa daga kudancin kasar Sin zuwa arewacinta da saukaka fatara a garuruwan da ke fama da talauci a yammacin kasar Sin da dai sauransu, kuma dukan wadannan na shafar zaman rayuwar jama'a sosai.

Bisa rahoton aikin da aka bayar a taron majalisar CPPCC ta 10, an ce, a cikin shekaru biyar da suka wuce, kashi 99% daga cikin shirye-shirye dubu 20 da 'yan majalisar suka gabatar sun sami karbuwa. A matsayinta na wakiliyar majalisar CPPCC, abin da ya fi faranta wa madam Wei Wei rai shi ne ta bayyana burin jama'a da bukatunsu ta hanyar ba da shawarwari ga gwamnati.

A unguwar Chang'an ta birnin Xi'an, babban birnin lardin Shanxi, akwai wani kauyen da ake kira "Jiuzhaizi", kuma iyalai 230 na zama a cikin kauyen. Rabin mazaunan kauyen suna gudanar da aikin kafinta. Amma sabo da lalacewar tsarin hanyoyin samar da wutar lantarki a kauyen, mazaunan kauyen sun yi fama da matsalar daukewar wuta sosai. Fang Hongsheng, wani mazaunin kauyen ya ce, "A cikin shekaru da dama da suka wuce, tsarin hanyoyin samar da wutar lantarki a barkatai suke, kuma yawan kayayyakin da ke aiki da wutar lantarki da suka lalace sakamakon tsarin ya wuce lisaftuwa, a kowane mako, akwai kwana uku ko hudu da aka sami daukewar wuta. Duk lokacin da aka sami bugowar iska ko ruwan sama, ba shakka, za a sami daukewar wuta."

A duk lokacin da wuta ta dauke, ba yadda za a yi sai a dakatar da aikin kafinta, wanda ya kawo illa ga kudin shiga ma mazaunan kauyen.

Sabo da haka, a farkon shekarar 2004, ta wata jaridar wurin ne, Fang Hongsheng ya sanar da Madam Wei Wei kan burinsa na sauye halin da mazaunan kauyen ke ciki.

Bayan da madam Wei Wei ta sami labarin, sai ita da kanta ta je wannan kauye don yin bincike, ban da matsalar samar da wutar lantarki, ta kuma gano lalacewar hanyoyi. Bayan haka, ta gano cewa, babu ruwan famfo a kauyen, mazaunan kauyen na ci gaba da amfani da rijiyoyin da aka haka a tsakanin shekarun 1070 zuwa na 1980 wajen samun ruwa. Madam Wei Wei ta gane cewa, idan ba a daidaita matsalolin ba, ba ma kawai mazaunan kauyen ba za su iya jin dadin zaman rayuwarsu ba, har ma aikinsu na kafinta zai iya lalacewa. Ta ce, "matsalolin hanya da wutar lantarki da kuma ruwa tsohuwar matsala ce a kauyen Jiuzhaizi. A game da matsalar, tun daga shekarar 2004, a gun taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin da kuma taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta lardinmu, sau da dama na yi kira da a mai da hankali a kanta ta hanyar yin jawabi da kuma gabatar da shirye-shirye."

Bisa binciken da aka yi, an gano cewa, ba ma kawai kauyen Jiuzhaizi shi kadai ke fama da matsalar samun wutar lantarki, wasu kauyukan sauran lardunan kasar Sin ma na fama da ita. Sabo da haka, a gun taron shekara shekara na CPPCC da aka kira a shekarar 2005, Madam Wei Wei ta gabatar da wani shirin da ke da lakabin "manoma na matukar bukatar gyaran tsarin hanyoyin samar da wutar lantarki", sa'an nan, a hukunce ne taron ya kula da shirin, kuma ya mika shirin ga majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta lardin Shan'xi da kuma hukumar birnin Xi'an. Daga baya, a watan Afril na wancan shekara, hukumar birnin Xi'an ta yanke shawarar ware kudaden jari, don gyaran tsarurrukan samar da ruwa da lantarki da kuma hanyoyi a kauyen Jiuzhaizi. Yanzu hali ya canza a kauyen, malam Fang Hongsheng, wani mazaunin kauyen ya ce, "bayan da aka gyara tsarin hanyoyin samar da wutar lantarki, yanzu kwayayen lantarki na ba da haske, hanyoyi na da fadi, ga shi kuma mazaunan kauyenmu suna iya amfani da ruwan famfo mai tsabta, kowa na da kuzari sosai."

Wakilin majalisar CPPCC ya kasance mutumin da ke daukar babban nauyi kuma mutumin da ke gudanar da aiki mai wahala. Amma duk da haka, a ganin madam Wei Wei, abin sa'a a gare ta shi ne, a gun taron shekara shekara na CPPCC, ta iya bayyana burin jama'a da kuma ba da shawarwari ga hukumomi daban daban da kuma sa kaimi ga daidaita wasu matsaloli.