Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 11:10:14    
Kada a sa siyasa a cikin wasannin Olympic

cri
Bisa labarin da kamfanin watsa labaru na kasar Amurka ya bayar a ran 13 ga wata, an ce, a gun taron wasannin motsa jiki na duniya da aka shirya a ran 12 ga wata a jihar California ta kasar Amurka, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Amurka Mr. Peter Ueberroth ya bayyana cewa, kara cudanya dake tsakanin mutane zai kyautata dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, yanzu, wasannin Olmpic tana yin muhimmin aikin nan.

Manyan jami'an sama da 500 daga sha'anin wasan motsa jiki da ciniki na duniya sun halarci taron. Game da wadansu zargi da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi wa kasar Sin, Mr. Ueberroth ya ce, idan an yi magana bisa ra'ayin hangen nesa, ya kamata su yi cudanya da kasar Sin da duk karfinsu. Ya yi kira ga masu halatar taron da su kara yin cudanya da kasar Sin da kuma samun abokai, a sa'I daya kuma, ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da kara karuwa.

Mr. Ueberroth ya jadadda cewa, kada a sa siyasa a cikin wasannin Olympic, yin adawa da wasannin Olympic zai kawo illa ga 'yan wasa. Ya ce, tilas ne kasar Sin za ta cimma nasarar shirya wasannin Olympic, kasar Sin za ta kara bude kofarta ta hanyar shirya wasannin Olympic. (Zubairu)