Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 16:34:32    
Kasar Sin tana gaggauta gina tsarin al'adu na bainar jama'a

cri

Ran 13 ga wata, a nan birnin Beijing, mataimakin ministan al'adu na kasar Sin Zhou Heping ya bayyana cewa, a shekarun nan da muke ciki, kasar Sin tana gaggauta gina tsarin al'adu na bainar jama'a, kuma ta sami nasara mai yawa.

Yayin da Mr. Zhou Heping yake zantawa da manema labaru na gida da na waje, ya bayyana cewa, a shekarun nan da muke ciki, kasar Sin ta dauki matakai da dama wajen raya al'adu na kasar, misali ta gina wasu sababbin labarare, da dakunan al'adu da dakunan baje-koli da dai makamantansu. Yawan kudin da aka zuba wajen sha'anin al'adu tana ta karuwa a ko wace shekara, tun daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2006, yawan kudin da aka zuba wajen sha'anin al'adu a ko wace shekara dukkansu sun karu da kashi 10 cikin kashi 100.(Bako)