Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 15:33:45    
Sababbin sana'o'i suna da ban sha'awa

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin ta bayar da sakamakon kididdigar da ta samu,inda ta bayyana cewa,kawo yanzu,gaba daya adadin sana`o`i na kasar Sin ya riga ya kai fiye da dubu daya da dari tara.Mun sami labari cewa,a cikin `yan shekarun da suka shige,tsarin sana`o`i na kasar Sin ya sami manyan sauye-sauye,sabbin sana`o`i da ire-iren ayyuka a jere wadanda suke dacewa da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al`umma sun bullo a kai a kai.

A shekara ta 1999,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin ta taba bayar da wani rahoto,inda ta nuna mana cewa,a wancen lokaci,adadin sana`o`i na kasar Sin ya riga ya wuce dubu daya da dari takwas da talatin,ire-iren ayyuka ma ya kai fiye da dubu takwas.A cikin `yan shekarun da suka shige,bisa bunkasuwar tattalin arzikin duk fadin duniya da kuma ci gaban kimiyya da fasaha,wasu sana`o`i da ire-iren ayyuka na gargajiya sun riga sun bace.A sa`i daya kuma,wasu sabbin sana`o`i kamarsu mai ba da shawara kan ciniki da mai aikin kwalliya ga mota da sauransu sun bullo.Dalilin da ya sa haka shi ne domin bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin tattalin arzikin kasuwanni na gurguzu,a kai a kai ne sha`anin ba da hidima ya sami bunkasuwa.Bisa sauye-sauyen tsarin tattalin arzikin kasa da ci gaban kimiyya da fasaha,tsarin sana`o`i na ayyukan ba da hidima shi ma ya sauya,saboda da haka,yawan mutane dake yin sabbin sana`o`i shi ma ya kara karuwa.

Don biyan bukatun zaman al`umma da kuma kyautata ingancin sabbin sana`o`i,a cikin shekaru biyar da suka shige,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin tsara ma`aunin sabbin sana`o`i 52.A shekarar bara,ma`aikatar nan ta kafa tsarin sanar da sabbin sana`o`i.Ya zuwa yanzu,gaba daya ma`aikatar ta riga ta sanar da sabbin sana`o`i 19 ga zaman al`umma,wadannan sabbin sana`o`i sun hada da sha`anin IT da sha`anin ba da shawara da sauransu.Dalilin da ya sa haka shi ne domin gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali kan sha`anin kera kayayyaki da sha`anin IT da sha`anin ba da hidima.A sa`i daya kuma,saboda ingancin zaman rayuwar jama`a ya sami kyautatuwa,shi ya sa wasu sana`o`i dake cikin sha`anin ba da hidima kamasu mai aikin jiyya ga lafiyar dabbobi da ake ajiye a gida da mai aikin kwalliya ga mota da sauransu sun fito.Ban da wannan kuma,bunkasuwar wasu sha`anonin kasar Sin ita ma ta kago muhalli mai kyau ga fitowar sabbin sana`o`i.Alal misali,a cikin `yan shekarun da suka shige,sha`anin taron nune-nune ya sami bunkasuwa cikin sauri a nan kasar Sin,wannan ya sa aikin ba da shawara kan shirya taron nune-nune ya zama wani sabon sana`a.Mun sami labari cewa,kawo yanzu,yawan masu ba da shawara kan shirya taron nune-nune a kasar Sin ya riga ya kai fiye da dubu daya.

Ban da wannan kuma,akwai sauran sabbin sana`o`i da yawa a kasar Sin,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin za ta ci gaba da sanar da su a nan gaba.