Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 15:30:23    
Bai kamata a sanya aikace-aikacen siyasa cikin wasannin Olympic ba

cri
Bisa labarin da jaridar "Le Figaro" ta kasar Faransa ta bayar a ran 11 ga wata, an ce, kwanan baya shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Mr. Rogge ya gana da wakilinta, inda ya ce, wasannin Olympic babban biki ne na dukkan mutanen duniya, bai kamata a sanya aikace-aikacen siyasa a cikin wasannin Olympic ba.

Mr. Rogge ya ce, a lokacin wasannin Olympic na Beijing, manema labaru sama da dubu 25 da suka zo daga kasa da kasa za su yi intabiyu a kasar Sin cikin yanci. Matsayin kwamitin wasannin Olympic na duniya a fili yake, 'yan wasa suna iya bayana ra'ayoyinsu cikin yanci, amma bai kamata su yi aikace-aikacen siyasa a wasannin Olympic ba. Wasannin Olympic biki ne na dukkan mutanen duniya, kada wadansu mutane su kawo illa gare shi. Mr. Rogge yana fatan cewa, ya kamata kowa ya nuna girmamawa ga mutuncin wasannin Olympic.

Ban da wannan kuma, Mr. Rogge ya bayyana cewa, kwamitin wasannin Olympic kungiyar wasannin motsa jiki ne kawai, ba kungiyar siyasa ba, nauyin da aka dora kan wuyansa shi ne shirya wasannin Olympic cikin lumana, da kuma taka rawa kan cudanyar dake tsakanin jama'ar kasashe daban daban. Idan ya shafi fannin siyasa, sai ya saba manufar nan. (Zubairu)