A ran 12 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dukufa kan raya sabuwar dangantakar abokantaka tsakaninta da Afirka bisa manyan tsare-tsare.
A gun taron manema labarai na gida da na waje da aka shirya a ranar a gun taron farko na majalisa ta 11 ta wakilan jama'ar kasar Sin, Mr. Yang ya bayyana cewa, kasar Sin ta mayar da kasashen Afirka a matsayin aminai ne cikin sahihanci, kuma tana dukufa kan raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Halayen musamman na dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka su ne sada zumunci cikin sahihanci, da yin zaman daidai wa daida, da nuna wa juna goyon baya, da kuma samun bunkasuwa gaba daya. Ba kawai hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya inganta bunkasuwar Afirka ba, har ma ya sa kaimi ga sauran kasashe wajen kara mai da hankali kan Afirka.
Ban da wannan kuma Mr. Yang ya ce, kasashen Afirka suna da hakkin zabar abokansu na hadin gwiwa bisa son ransu, kuma suna da hakkin samun bunkasuwa ta yin amfani da albarkatunsu da kuma sauya boyayyen rinjayensu zuwa na zahiri ta hanyar hadin gwiwa.(Kande Gao)
|