Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 09:19:26    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(06/03-12/03)

cri
Ran 8 ga wata bisa agogon wurin, a kasar Jordan, a bakin tekun Dead Sea, a lokacin da yake halartar babban taro kan harkokin mata da wasannin motsa jiki na kasa da kasa a karo na 4, Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa wato IOC ya bayyana cewa, kasar Sin ta sami babban ci gaba a fannin yin kokarin kyautata ingancin iska kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008. Wannan shugaba ya kuma yi karin bayani kan dimbin matakan da kasar Sin take dauka domin kyautata ingancin iska da tinkarar gurbata muhalli. Ya kuma kyautata zaton cewa, ingancin iskar Beijing zai sami kyautatuwa daga dukkan fannoni kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Ran 5 ga wata, a nan Beijing, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya yi nuni da cewa, a galibi dai an kammala gina kauyen wasannin Olympic, wanda zai ba da kyawawan hidimomin abinci da wuraren kwana ga 'yan wasa da malaman horas da wasanni da kuma jami'ai masu shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing da ta nakasassu. Wannan kauyen wasannin Olympic na cikin kusurwa ta arewa maso yammacin wurin yawon shakatawa na wasan Olympic, fadinsa ya kai kadada misalin 66, ya hada da gine-gine 42 da kuma cibiyar ba da hidima. Madam Liu Rong, wakiliyar mai gina kauyen ta bayyana cewa, yanzu an riga an gama kayatar da gine-ginen a ciki da kuma a waje, haka kuma, an jarraba tsare-tsaren ba da wutar lantarki da samar da ruwa da injunan sanyaya daki. Ban da wannan kuma, an dora muhimmanci kan yin amfani da makamashin da ake iya sake amfani da shi da yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli a lokacin da ake gina wannan kauye.

A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasa da jami'ai fiye da dubu 16 za su zama a kauyen wasan Olympic. Bayan gasar, za a sayar da gidajen da ke kauyen zuwa mazauna birnin Beijing.

Kwanan baya, a nan Beijing, Yu Chunquan, shugaban sashen zirga-zirga na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, dukkan motoci da hidimomin zirga-zirga da za a samar wa ma'aikatan da suka yi rajista, kamar su jami'ai da 'yan wasa da dai sauransu, za su biya bukata wajen 'shirya gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba'.

Ran 9 ga wata, a birnin Valencia na kasar Spain, a cikin karon karshe na shirin gudun ketare shinge mai tsawon mita 60 na gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta shekarar 2008 a cikin daki, dan wasa Liu Xiang na kasar Sin ya zama zakara da dakika 7 da motsi.(Tasallah)