Saurari
"Muna fama da matsalar karancin makamashi, kuma muna fuskantar hali mai tsanani a fannin kiyaye muhalli."
Ba a rasa sauraron irin wannan furuci ba a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin da aka kira a cikin shekarun baya. A gun tarurrukan biyu na wannan shekara da ake gudanarwa a halin yanzu ma, yadda za a yi tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu guba, don kara kiyaye muhallin zama, sun sake zama abin da ke jawo hankulan mahalartan tarurrukan biyu.
Tuni Sin ta fara daukar matakan tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba, don kiyaye muhalli. Gwamnatin kasar Sin ta kafa tsarurrukan sa ido da bincike a fannin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba, ta kuma kara gyara tsarin masana'antunta.
Hukumomin wurare daban daban su ma suna mai da hankulansu sosai a kan aikin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba. Mr.Xu Shousheng, wani wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma shugaban lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, ya ce,"mun kara karfin rufe wasu masana'antun da ke gurbata muhalli sosai da kuma bukatar makamashi sosai. Mun rufe kananan masana'antun yin takardu da kananan masana'antun sarrafa bakin karfe da kuma wasu kananan masana'antun yin sumunti, bayan haka, mun kuma rufe wasu kananan mahakan kwal fiye da 1300 da ba su iya ba da kariya da ma'aikatansu ba."
Ban da masana'antu, ra'ayin tsimin makamashi ya kuma zauna da gindinsa a zukatan Sinawa. Madam Zhao Yingchun, wata mazauniyar birnin Beijing ta sami ilmi da yawa dangane da tsimin makamashi daga shirin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba da aka gudanar a tsakanin dukan jama'ar Sin. Yanzu tsimin makamashi ya zamo mata al'ada ta zaman yau da kullum. Ta ce,"A da, mu kan yi amfani da babban kwan lantarki a gidanmu, amma bayan na shiga shirin, yanzu kusan ba mu yin amfani da babban kwan lantarki a dare, a maimakonsa, wani karamin kwan lantarki ne muke amfani da shi, kuma mu kan rufe shi da zarar mun fita waje. A ganina, tsimin ruwa da wutar lantarki da rage amfani da mota kwana daya a ko wane wata, zai iya rage fitar da iskar Carbon Dioxide, wanda zai amfana wa lafiyar jikinmu. Musamman ma za a gudanar da wasannin Olympics a shekarar da muke ciki, ya kamata mu karfafa wannan ra'ayi na tsimin makamashi."
Hakar kasar Sin ta cimma ruwa. Misali a nan birnin Beijing, yawan kwanakin da ake iya samun launin shudi a sararin samaniya ya karu daga 100 a shekarar 1998 zuwa 246 a shekarar bara. Amma duk da nasarorin da ta samu, akwai kuma wasu matsalolin da ba a iya kyale su ba. A gun taron manema labarai da aka kira a yau, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin raya kasa da yin gyare-gyare, Mr.Xie Zhenhua ya yi nuni da cewa, a shekarar da muke ciki, za a kara karfin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli. Sa'an nan, a cikin rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya gabatar a gun bikin bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya jaddada cewa, kamata ya yi a gaggauta aikin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba. Ya ce,"za mu sa kaimi ga jama'a da su yi kokarin raya zaman al'umma da ke tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli, kuma ya kamata mu tsaya kan tsimin makamashi da kiyaye muhalli zuriya bayan zuriya, ta yadda za mu kara mayar da tsaunukanmu su zama kore shar, ruwanmu ya zama mai tsabta, kuma sararin samaniya ya zama mai shudi."(Lubabatu)
|