Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 21:51:03    
Tattalin arzikin kasashen Afirka yana da kyukkyawar makoma

cri

Bisa bayanan tattalin arziki mai dumi-dumi da kasashen Afirka suka bayar, yanzu tattalin arzikin kasashen Afirka yana cikin hali mafi kyau da ba a taba gani ba a tarihi. Ban da wasu kasashe kalilan, yawancin kasashen Afirka sun shiga wani sabon zamani na bunkasuwar tattalin arziki lami lafiya.

A kwanakin baya, mujalla mai suna "bayyanai kan kasuwanci da fasaha na kasashen Afirka" ta buga wani bayani wanda ya ruwaito hukumar ba da lamuni ta duniya ta IMF na cewa, yanzu kasashen Afirka suna cikin "zamani mafi kyau na samun bunkasuwa mai dorewa rashin hauhawar kudi".

A cikin shekaru 5 da suka wuce, saurin karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka ya kai fiye da kashi 5 cikin 100 a kiyasce, har ma a cikin shekarar 2007, wannan ya kai kashi 6.2 cikin 100. bisa bayanan hukumar ba da lamuni ta duniya ta IMF, tun daga shekarar 1997 zuwa shekarar 2002, matsakaicin yawan kudin da ko wane mutumin kasashen Afirka ya samu daga wajen samar da kayayyaki a ko wace shekara ya karu da kashi 1 cikin 100 a kiyasce, amma tun daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2007, wannna ya karu zuwa kashi 3,6 cikin 100.

Akwai yawan dalilan da suka sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Affirka. Da farko, a cikin shekarun baya, kasashen Afirka da yawa suna tafiyar da manufar tattalin arziki bisa kasuwanci, suna kirkiro wani hali mai kyau wajen zuba jari.

A cikin shekarun baya, mutane da yawa sun zuba jari mai yawa a kasashen Afirka ta kudu, da Nijeriya, da Ghana, da Kenya, da Uganda, da Zambia da sauran kasashen Afirka. Manyan dalilai su ne, wadannan kasashen suna tafiyar da manufar tattalin arziki mai sassauci, kuma sun sami cigaba wajen kyautata manyan ayyuka. Manyan sana'o'in da aka zuba jari su ne makamashi, da yawon shakatawa, da bankuna.

Bisa kididdigar da taron neman bunkasuwa da yin cinikiya na majalisar dinkin duniya ya yi, yawan jarin da aka zuba a Afirka kai tsaye ya kai dolar Amurka biliyan 40. Masu bincike sun kiyasta cewa, wannan zai karu zuwa dolar Amurka biliyan 100 a shekarar 2010.

Ban da haka kuma, a cikin shekarun baya, kasashen duniya sun samu karuwar bukatu kan man fetur da ma'adinai da sauran kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa kasashen waje, wannan ya sa kaimi ga kasashen Afirka da su kara fitarwa kayayyakinsu. A cikin shekarun baya, bisa kididdigar da aka yi, yawan darajan kayayyakin da kasashen Afirka suka fitar da su zuwa kasashen waje ya karu daga dolar Amurka biliyan 182 na shekarar 2004 zuwa dolar Amurka biliyan 293 na shekarar 2006.

Ban da haka kuma, an sami kwanciyar hankali a wasu kasashen da suka taba zama cikin yaki har na dogon lokaci, wannan ya ba da sharradi mai kyau ga bunkasuwar tattalin arziki. Sauran dalilan da suka sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki sun kunshi kyautattuwar manyan gine-gine, da ingantattun hanyoyin sarrafa tattalin arziki, da halin tattalin arziki mai kyau na kasashen duniya.

A galibi dai, a cikin shekarun baya, kasashen Afirka sun sami bunkasuwar tattalin arziki mai karko. Amma a sa'I daya kuma, suna fuskantar wasu matsaloli.

Dandalin tattalin arzikin kasa da kasa ya taba yin gargadi cewa, kasashen Afirka sun sami cigaba saboda "karuwar farashin kayayyaki, da kuma an yafe musu basussukansu, da halin tattalin arziki mai kyau na duniya", amma idan Afirka suna son samun bunkasuwa mai dorewa a zahiri, to, dole ne su kafa tushen tattalin arziki mai karko a gida, wannan ya hada da sauya hanyoyin bunkasuwa, da cigaba da kyautata manyan gine-gine.

Hukumar ba da lamuni ta duniya ta IMF tana yi wa tattalin arzikin Afirka hangen kyakkyawar makoma a shekarar da muke ciki, ta kiyasta cewa, watakila saurin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka zai kai kashi 6.5 cikin 100. amma, wasu gwanayen tattalin arziki suna ganin cewa, mai yiyuwa ne rikicin ba da lamunin gidaje na kasar Amurka zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin Afirka.(Musa)