A gun taron manema labaru da aka shirya a yau ranar 11 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang, ya bayyana cewa, tun bayan da birnin Beijing ya samu nasara wajen samun damar shirya wasannin Olympic, kasar Sin ta dauki matakai sama da 200, don kyautata muhalli, sakamakon haka ingancin yanayi ya samu kyautatuwa sosai. Kasar Sin na da niyyar gabatar da wani kyakkyawan muhalli mai tsabta a lokacin wasannin Olympic na Beijing.
Bugu da kari kuma, Mr. Qin Gang ya ce, yanzu bangarori daban daban da abin ya shafa suna tabbatar da matakan tsaro na wasannin Olympic na Beijing a dukkan fannoni. Gwamnatin kasar Sin za ta sanya matukar kokari wajen gudanar da ayyukan tsaro iri daban-daban na gasar wasannin Olympic ta Beijing, ta yadda za a ba da tabbaci ga gudanar da wannan gagarumar gasa lami lafiya. (Bilkisu)
|