Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 16:55:33    
Kafofin yada labaru na kasashen ketare sun sa lura sosai a kan taruruka biyu na Sin

cri

Kwanakin nan, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun ci gaba da sa lura sosai a kan zama na farko na majalisar wakilan jama'a ta karo na 11 ta kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma an mai da hankulan sosai a kan matakan kyautata zaman rayuwar jama'a da kasar Sin ta dauka kan yaki da bambamcin tsakanin masu arziki da matalauta, da inganta ba da tabbaci ga taimakon jama'a a zamantakewar al'umma.

Jaridar safiya ta hadin gwiwa ta kasar Singapore ta bayyana cewa, hukumar shari'a ta kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali sosai wajen samar da sabon wurin zama ga mutane da ba da ingancin abinci da ba da ishora a zamantakewar al'umma, da tabarbarewar muhallin halittu da dai sauransu.

Jaridun Jamus sun bayar da takaitaccen bayyani kan rahoton aikin gwamnatin da firaministan Sin Mr Wen Jiabao ya yi, kuma sun sa lura sosai wajen hauhawar farashin kayayyaki da kuma bambamcin tsakanin masu arziki da matalauta da aka ambata a cikin rahoton, kuma an gabatar mana da wasu matakan da aka dauka wajen kara inganta aikin jinya da ba da ilmi da kuma kasafin kudi ga jin dadin rayuwar jama'a a zamantakewar al'umma.

Kafofin yada labaru na kasar Birtaniya da Rasha da Cuba su ma sun bayar da labaru game da taruruka biyu na Sin, kuma sun sa lura sosai a kan rahoton gwamnatin da firaministan Sin Wen Jiabao ya yi.(Bako)