Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 16:11:29    
Za a bada tabbaci ga ingancin iska a yayin gasar wasannin Olympics ta Beijing, in ji wani mai fafutukar kiyaye muhalli na Sin

cri

Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, mataimakin shugaban babbar hukuma mai fafutukar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhang Lijun ya bayyana yau 11 ga wata a nan birnin Beijing cewar, za a tabbatar da ingancin iskar Beijing a yayin gasar wasannin Olympics ta Beijing wadda za a shirya nan ba da dadewa ba.

A wajen taron manema labaru da zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 ya shirya a ranar, yayin da Mr. Zhang ke amsa tambayoyin manema labaru, ya yi nuni da cewar, tun daga shekarar 1998, an fara dukufa ka'in da na'in wajen yin rigakafi da shawo kan gurbacewar iska. Bayan da birnin Beijing ya cimma nasara a wajen takarar neman izinin shirya gasar wasannin Olympics a watan Yuli na shekarar 2001, hukumarsa ta rubanya kokarin yin rigakafi da magance wannan matsala. Zuwa yanzu, an rigaya an kammala harkokin yin rigakafi da shawo kan gurbacewar iska da yawansu ya zarce 200, yawan jarin da aka zuba cikin wadannan ayyuka sun wuce kudin Sin Yuan biliyan 120. A sanadin irin matukar kokarin da aka yi, ingancin iskar Beijing ya kyautatu kwarai.

A waje daya kuma, Mr. Zhang ya ce, domin bada cikakken tabbaci ga ingancin iskar Beijing a yayin gasar wasannin Olympics, kamata ya yi a dauki matakai cikin hadin-gwiwa tsakanin wurare daban-daban dake kewaye da Beijing, da yin rigakafi da shawo kan gurbacewar iska daga dukkan fannoni.(Murtala)