Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 12:26:14    
Kai ziyara ga gandon noma na nishadi mai suna Lvguang a tabkin Taihu a birnin Suzhou

cri

Gandun noma na nishadi na Lvguang mai fadin kadada misalin 30 yana kusa da dutsen Xishan na birnin Suzhou, shi ne gandun noma na farko da ake iya samar da amfanin gona da yada zango da kuma yin yawon shakatawa a ciki. An raba gandun noma zuwa sassa daban daban, kamar farfajiyar noman 'ya'yan itatuwa da wurin kiwon dabbobi da kuma dakuna da aka rufe da leda don yin noma. Mai gandun noman Cai Shengjia ya ji alfahari sosai ya gaya mana cewa, an tara ruwan sama ta hanyar na'urorin musamman. Bayan da aka sarrafa ruwan saman, ana yin amfani da shi domin yin wa kayan lambu da 'ya'yan itatuwa ban ruwa, ta haka wadannan kayan lambu da 'ya'yan itatuwa da aka samu a gandun nomansa suna da dadin ci sosai. Ya ce,

'Ga misali, an yi amfani da takin zamani wajen noman kokwamban da ake sayarwa a kasuwa. Amma na iya tabbatar da cewa, ba mu yin amfani da irin takin zamani wajen noman kokwamba a gandun nomana ba. Saboda amfanin gona da ba a iya amfani da taki zamani ko magungunan kashe kwari ba wajen nomansu suna fi dadin ci, kuma suna kunshe da ruwa kwarai. A takaice dai, in wani ya ci, to, zai gane cewa, wadannan kokwamba sun sha bamban sosai da saura.'

Bisa fasahohin da aka samu a can da, dimbin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa suna girma sosai a lardin Taiwan, amma ba su saba da yanayi da kasa a babban yankin kasar Sin ba. Shi ya sa yadda za su saba da babban yankin kasar Sin ya zama wata matsala, amma hakan bai dami malam Cai ba, yana mallakar fasahohi da yawa. Ya ce,

'Yawancin amfani gona ana kai su zuwa lardin Taiwan daga babban yankin kasar Sin ne a can can can da. Mun yi amfani da fasahohinmu wajen sanya su saba da muhallin Taiwan sannu a hankali, shi ya sa na taba gabatar da su ga dimbin manoma. Ko da yake an yi noman amfanin gona iri daya a wurare masu layin iri daya da ya zagaye duniya tare kuma da zafin yanayi iri daya, ana kuma yi nomansu ta hanya iri daya a babban yankin kasar, amma a karshe dai, dandadinsa ya canza. Dalilin da ya sa hakan shi ne domin irin wannan amfanin gona bai saba da wurin da ake nomansu ba. Yanzu mun fito da dabarar sanya amfanin gona su saba da wuraren da ake nomansu cikin sauri.'

Malam Cai ya kara da cewa, yanzu Taiwan ba ta da boyayyen karfi wajen ci gaba da raya aikin gona na nishadi ba, amma babban yankin Sin ya shiga mataki na farko wajen raya irin wannan sana'ar da abin ya shafa, yana da babbar kasuwa. Yana kasancewa da babban karfin saye-saye a yankin kogin Yangtse Delta, shi ya sa wannan yanki ya dace da raya aikin gona na nishadi.

Fasahar aikin gona ta lardin Taiwan ta fi ta babban yankin Sin zamani, wannan shi ne daya daga cikin dalilan da ya sa babban yankin Sin yana maraba da 'yan kasuwa na Taiwan su zuba jari kan aikin gona irin na yawon shakatawa. Wu Wenyuan, mataimakin darektan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar birnin Suzhou ya bayyana cewa, 'yan kasuwa na Taiwan ba kawai sun kawo tunanin zamani kan raya gandun noma na nishadi ba, har ma sun kawo fasahohin zamani na Taiwan kan tafiyar da aikin gona. Wu ya ce,

'Tabbas ne kafuwar gandun noma na nishadi na Lvguang da kuma kaddamar da shi za su sa kaimi kan samun nasarar yin gyare-gyare kan aikin gona a tsibirin dutsen Xishan har ma a dukan yankin tabkin Taihu na Suzhou, ta haka aikin gonan zai sami saurin bunkasuwa. Gandun noma mai suna Lvguang zai zama muhimmin abin koyi wajen hada aikin gona na zamani da aikin ba da hidima a harkokin yawon shakatawa tare. Sa'an nan kuma, samun nasarar kafa gandun noma mai suna Lvguang da kuma kaddamar da shi sun samar da dandamali da kuma misali wajen yin hadin gwiwa da bunkasa aikin gona da aikin yawon shakatawa a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma za su daukaka mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2 a dukan masana'antu.'(Tasallah)