
Yau a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kamata a kara inganta tsaron kasa da raya rundunar sojoji, don kara ba da taimako ga tabbatar da tsaron kasa da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya.

Mr.Hu Jintao ya yi wannan furuci ne a yayin da yake halartar cikakken zaman wakilan rundunar sojojin 'yantar da jama'a a gun taron wakilan jama'a a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11. Ya ce, a yayin da ake raya tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'umma daga dukan fannoni, tilas ne a kara inganta tsaron kasa da raya rundunar sojoji, don samar da tallafi da tabbaci ga bunkasa gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin, da kuma kara ba da taimako ga kiyaye zaman lafiyar duniya.(Lubabatu)
|