Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 19:19:09    
Batun yaki da cin hanci da rashawa ya fi janyo hankulan wakilai mahalartan tarurrukan majalisu biyu da ake gudanarwa a kasar Sin

cri

Saurari

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a yanzu haka dai, ana gudanar da taron shekara-shekara na hukumar koli ta mulkin kasar Sin wato majalisar wakilan jama'ar kasa a nan birnin Beijing. Ko fararen hula ko kusoshin gwamnatin kasar dukkansu sun ce, taron nan da ake gudanarwa, wani taro ne na sauraron ra'ayoyin jama'a, wadanda suka fi mai da hankali kan wassu batutuwa, musamman ma batun yaki da cin hanci da rashawa. Wani tsoho mai suna Li Wenxing ya fada wa wakilinmu cewa: " Aikata laifin cin hanci da rashawa da ake yi, abu ne da ya fi yin illa ga babbar moriyar jama'a masu tarin yawa na kasarmu da kuma lahanta kwarjinin gwamnatin kasar. Saboda haka ne dai, mu fararen hula muna kyamar irin wannan laifi da wassu mahukunta sukan barkata".

Wakilai mahalartan taron sun bayyana koke-koken fararen hula a gaban taron, inda wakilan suka fadi albarkacin bakinsu kan yadda yanke hukunci mai tsanani kan masu aikata laifin cin hanci da rashawa, da magance aukuwar lamarin cin hanci da rashawa da kuma bada tabbaci ga gudanar harkokin gwamnatin kasa ba tare da yin rufa-rufa ba. Mr. Deng Chuan, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasa kuma shugaban hukumar ladabtarwa ta jama'a ta lardin Sichuan yana mai cewa: ' Idan ba a tafiyar da ayyukan yaki da cin hanci da rashawa da kyau ba, to labuddah hakan zai yi mummunan tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki da kuma jituwar zamantakewar al'ummar kasar'. A nasa bangaren, wakili daga kotun koli ta jama'a ta lardin Hunan, Mr. Kang Weimin ya furta cewa : ' Kowa da kowa na yin zaman daidai wa daida a gaban shari'a'.

Game da koke-koken wakilai mahalartan taron, gwamnatin kasar Sin ta mayar da martani a tsanake a kai. Mr. He Guoqiang, wakilin din-din-din na ofishin siyasa na kwamtin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma sakataren kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya sake bayyana aniyar yaki da cin hanci da rashawa. Yana mai cewa: ' Wajibi ne a nace ga daukar tsauraran matakai don yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka barkata laifuffukan cin hanci da rashawa. A shekarar da muke ciki, muhimmin aikin dake gabanmu shi ne yanke hukunci kan halayya maras kyau dake lahanta babbar moriyar jama'a da kuma daidaita maganganu dake shafar wassu mahukunta wadanda suka yi abubuwa marasa da'a da kuma kaddamar da wani cikakken tsarin yaki da cin hanci da rashawa da daukaka yunkurin gyare-gyare na zahiri'.

Lallai gwamnatin kasar Sin ta gane sosai kan yadda za ta dakile abubuwan cin hanci da rashawa da wassu mahukunta suke yi, wato ke nan tana tsayawa kan matsayin yaki da cin hanci da rashawa yayin da take daukar kwararan matakai na gudanar da wannan babban aiki da kyau.

A gun rahoton aiki da shugaban kwamitin koli na ladabtarwa na jama'ar kasar Sin Mr. Jia Chunwang ya gabatar a gaban taron majalisar wakilan jama'ar kasar da aka gudanar a yau Litinin, ya furta cewa : ' Cikin shekaru biyar da suka gabata, an yi nasarar binciko batutuwan shari'a da yawansu ya kai 35,255 dake shafar mahukunta 13,929 wadanda suka kwashe dukiyoyin jama'a da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan daya'.

Jama'a masu sauraro, an kafa hukumar magance cin hanci da rashawa ta kasar Sin a watan Satumba na shekarar bara. Shugabar hukumar din Madam Ma Wen ta bayyana makasudin aikin hukumar. Tana mai cewa 'Kafa hukumar musamman ta yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin kasar, zai taimaka ga gudanar ayyukan cin hanci da rashawa yadda ya kamata. An yi haka ne domin biyan bukatun gudanar da wannan babban aiki da kuma sauye nauyin dake bisa wuyan hukumar na aiwatar da ' Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa'. ( Sani Wang)