Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 17:28:24    
Malam Gerke Roland, babban darektan rukunin kamfanonin Bosch da Siemens a kasar Sin

cri

Rukunin kamfaninin kera na'urorin da ake amfani da su a gidaje na Bosch da Siemens wani shahararrren rukuni ne a duniya, yawan kudin da yake samu daga wajen sayar da na'urorinsa a ko wace shekara ya kai matsayi na farko a nahiyar Turai, kuma ya kai matsayi na uku a duk duniya gaba daya. Wannan rukuni ya fara gudanar da harkokinsa a kasar Sin a shekarar 1994, kuma ya yi ta samun bunkasuwa kamar yadda ya kamata. A kwanakin baya, wakilin gidan rediyinmu ya kai ziyara ga malam Gerke Roland, babban daraktan rukunin a kasar Sin don jinta bakinsa dangane da ci gaban da rukuninsa ke samu a kasar Sin.

A babban zauren rukunin da ke a birnin Nanjing, fadar gwamnatin lardin Jiangsu a gabashin kasar Sin, Malam Gerke Roland ya bayyana wa wakilin gidan rediyonmu cewa, "ci gaban da muke samu a kasar Sin yana da muhimmanci ga rukuninmu, daidai kamar yadda tattalin arzikin kasar Sin yake da muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Mun yi matukar farin ciki da ganin irin ci gaban da muke samu wajen gudanar da harkokinmu a ko wace shekara. Sabo da haka mun hakake a sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, rukunin kamfanonin Bosch da Siemens shi ma zai kara samun ci gaba wajen gudanar da harkokinsa a kasar."

Ya zuwa yanzu dai, rukunin kamfanonin Bosch da Siemens ya riga ya kafa ma'aikatai uku masu kera na'urorin da ake amfani da su a gidaje da wani kamfanin sayar da na'urorin a kasar Sin. Yawan ma'aikatan da suka dauka ya wuce dubu 7, haka kuma tsarin sayar da na'urori na rukunin ya shafi birane da garuruwa da yawansu ya wuce 600. A zahiri dai, rukunin ya sami kaso mai yawa na irin wadannan na'urorin da ake sayarwa a kasuwannin kasar Sin.

Da Malam Gerke Roland ya tabo magana a kan dalilan da suka sa rukuninsa ya kafa babban zaurensa a birnin Nanjing, sai ya bayyana cewa, "dalilan da suka sa muka zabi birnin Nanjing don kafa babban zauren rukuninmu a kasar Sin su ne domin birnin Nanjing wani birni ne mai muhimmanci sosai a tsakiyar kasar Sin. Musamman ma birnin wata cibiyar ba da ilmi ce a kasar, a nan akwai shahararrun jami'o'i da yawa, don haka ana iya samun kwararrun ma'aikata masu yawa." A hakika, rukunin Bosch da Siemens ya ci gajiyar kwararrun ma'aikata masu yawa da ake samu a birnin Nanjing. A ganin Malam Gerke Roland, raya rukunin ma'aikata yana da muhimmanci sosai ga masana'antu.

Yanzu, manyan samfurori biyu kamar Bosch da Siemens na rukunin kamfaninin kera na'urorin da ake amfani da su a gidaje na Bosch da Siemens sun riga sun sami karbuwa sosai daga wajen masu saya. Daga katunan sunayen masu sayan kaya, wakilin gidan rediyonmu ya sami adireshen malam Shen Kuang, tsohon mai sayan na'urorin rukunin da ake amfani da su a gidaje, kuma ya bakunci gidansa. A cikin bayan gidansa, wakilinmu ya ga wani na'urar wanke tufafi wadda ko da yake salonta iri ta tsohuwa ce, amma duk da haka tana da kyan gani. Malam Shen Kuang ya bayyana wa wakilinmu cewa, "na yi kimanin shekaru 10 ina amfani da wannan na'urar wanke tufafi da kyau sosai. Na kan yi amfani da na'urar wajen wanke zanin gado da sauran manyan tufafi. Na'urar ta iya biya bukatuna wajen wanke tufafi. Ni ina sha'awar wasan motsa jiki kwarai. Don haka na kan sa takalma da sauransu a cikin na'urar don wanke su. Na'urar kuma tana wanke su da kyau sosai."

Malam Gerke Roland yana nuna cikakken imani ga makomar rukunin kamfanoninsa a kasar Sin, sabo da kyakkyawar fasahar rukunin da karbuwar da yake samu daga wajen masu saya da kuma na'urori masu dimbin yawa da ake bukata nan gaba a kasuwannin sayar da na'urori da ake amfani da su a gida.(Halilu)