
Ran 10 ga wata, a nan birnin Beijing, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Mr. Wu Dawei ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu shugabannin kasashen waje da kusoshin gwamnatoci fiye da 100 sun riga sun bayyana cewa za su halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing ta shekarar 2008.
Yayin da Mr. Wu Dawei yake zantawa da manema labaru na gida da na waje ya bayyana cewa, a ko wace rana, wannan adadi yana ta kara karuwa.
Tare da karatowar bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing, shugabannin kasashe da dama sun tabbatar da cewa za su nuna goyon baya ga gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing.

Wu Dawei ya bayyana cewa, gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing za ta kasance wani gaggarumin biki ne wajen motsa jiki ga duk mutanen duniya, haka kuma shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing cikin nasara shi ne babban buri na dukkan mutanen duniya.
Ran 8 ga watan Agustan, za a bude gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta karo na 29 ta Beijing. Haka kuma Beijing za ta shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta nakasassu. Gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a yi a wannan gami za ta zama wata gasar wasannin da kungiyar wakilan motsa jiki ta Sin ta tura 'yan wasanni mafi yawa don halartar gasanni mafi yawa a cikin dukkan tarihin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic.(Bako)
|