A ran 7 ga wata, daya bayan daya Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da sauran shugabannin kasar suka shiga tarurukan tattaunawa da wasu kungiyoyin wakilai masu halartar taron shekara-shekara na sabon zama na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin suka shirya a birnin Beijing.
Mr. Wu Bangguo ya shiga tarurukan tattaunawa da kungiyoyin HongKong da Macao suka shirya, inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana yin namijin kokari wajen goyon bayan ayyukan gwamnatocin yankunan musamman na HongKong da Macao, kuma tana tsayawa tsayin daka kan manufofin "kasa daya amma tsarin mulki biyu" da kuma "mazaunan Hong Kong da na Macao suna tafiyar da harkokinsu da kansu" domin ciyar da ayyukan raya yankunan biyu zuwa gaba.
Lokacin da firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ke halartar taron tattaunawa da kungiyar wakilan lardin Guangdong ta shirya, ya bayyana cewa, bayar da 'yancin ra'ayi abu mai muhimmanci ne wajen raya gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin. Lardin Guangdong wuri ne na farko wajen bin manufar bude kofa ga waje da kuma yin gyare-gyare a gida ta kasar Sin, shi ya sa ya kamata ya ci gaba da tsayawa a gaba a wannan fanni kuma aikin raya kasa mai zamani.(Kande Gao)
|