Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 19:11:07    
Kasar Sin za ta ba da tabbaci ga samar da ingantaccen abinci a wasan Olympic

cri

Ran 6 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Li Changjiang direkatan hukumar sa ido kan ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin ya nuna cewa, ko shakka babu, kasar Sin za ta ba da tabbaci ga samar da ingantaccen abinci a taron wasannin Olympic.

Yayin da Mr. Li Changjiang ke ganawa da manema labaru ya ce, gwamnatin kasar Sin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun kafa tsarin sa ido kan ingancin abinci a dukkan fannoni. Kyakkyawan masana'antun da aka zabi za su samar da dukkan abincin taron wasannin Olympic, kuma tilas ne halayen da suke ciki su dace da ma'aunin kasashen duniya. A sa'i daya kuma, dole ne dukkan abinci za su dace da jarrabawar hukumomin da abin ya shafa. Ban da haka kuma, kasar Sin za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa, da yin musanya tare da kamfannoninsu domin ba da tabbaci ga samar da ingantaccen abinci.