Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 19:16:38    
Ana gudanar da harkokin raya demokuradiyya da siyasa cikin taka tsantsan a kasar Sin

cri

Saurari

Madam Hu Shaoyan, wata manomiya ce mai shekaru 34 da hauhuwa na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Yau da shekaru goma da suka gabata, Madam Hu ta bar garinta zuwa lardin Guangdong daya daga cikin yankuna da suka fi samun bunkasuwar tattallin arziki a kasar Sin domin cin rani. Lallai ba ta taba yin tsammani ko da a cikin mafarki ba cewa ta zama daya daga cikin wakilai na sabuwar hukumar koli ta mulkin kasar wadda wa'adinta shekaru biyar ne. Ana iya cewa, wannan dai, wani muhimmin lamari ne dake cikin yunkurin raya demokuradiyya da siyasa a kasar Sin.

Tun bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata, ta samu bunkasuwar tattalin arziki da saurin gaske. Tare da kyautatuwar sana'o'in da ake yi, manoma masu tarin yawa sun bar garinsu zuwa birare domin neman aikin yi. Hakan ya zamanto rukunin "Manoma 'yan ci rani". Bisa 'yar kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi an ce, a yanzu haka dai, kasar Sin na da manoma 'yan ci rani da yawansu ya kai kimanin miliyan 130, wadanda akasarinsu suke yin aikin sana'o'in gine-gine, da kere-kere da kuma na sufuri da dai sauran makamantansu.Ko shakka babu wadannan manoma 'yan ci rani sun kasance wani muhimmin kashi dake cikin ma'aikan sana'o'i na kasar Sin sakamakon muhimmiyar rawa da suke takawa a fannin raya birane da kuma bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar. Da yake kasar Sin na kasancewa tamkar wani 'inji' ne na inganta ayyukan bunkasa tattalin arzikin duniya, shi ya sa ake iya cewa manoma 'yan ci rani na kasar Sin su ma sun bada taimako ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Amma domin har wa yau dai ana aiwatar da tsari iri biyu na rajistan iyalai a birane da kauyuka a kasar Sin, saboda haka , manoma 'yan ci rani suka fi mazauna birane shan wahalhalu a fannin samun ilmi, da jinya,da gidajen kwana, da kudin inshora da kuma aikin yi da dai sauran fannoni na zaman yau da kullum. A lokaci guda, wassu hukumomi da kamfanoni sukan taka wasu iko da moriya na halal na manoma 'yan ci rani, wadanda ba su da zurfin ilmi musamman ma a fannin shari'a.

Jama'a masu sauraro, manoma 'yan ci rani sun zama wakilai na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadanda za su tafiyar da harkokinsu bisa kundin tsarin mulkin kasar da kuma bada hannu ga tsara muhimman manufofin siyasa na kasar kai tsaye. Hakan ka iya kiyaye iko da moriya na halal na manoma 'yan ci rani da kuma bayyana halin demokuradiyya na tsarin majalisar wakilan duk kasar daga dukkan fannoni.

Aminai 'yan Afrika, abin da muka fi son nunawa, shi ne tun ba yau ba ne kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya demokuradiyya da siyasa, haka kuma ba za a tsayar da yin haka ba a yau. Tuni a shekarar 2002 lokacin da ake kiran babban taron wakilai na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, akwai masu masana'antu masu zaman kansu da yawa da suka zama wakilai na jam'iyyar din ; Ban da wannan kuma, a shekarar 2005, masu masana'antu masu zaman kansu sama da 30 da kuma manoma 'yan ci rani 23 sun yi alfaharin zama 'yan takarar ' Nagartattun 'yan kwadago na duk kasa'.

Ana kyautata zaton cewa, yawan wakilai manoma 'yan ci rani zai samu karuwa a nan gaba ; Kuma ana kyautata zaton cewa, za a dakatar da ikirarin cewa 'manoma 'yan ci rani' bayan gyare-gyaren manufar tsarin rajistan iyalai da kuma ci gaban yunkurin bunkasa masana'antu na zaman takewar al'ummar kasar.

Babu tantama, a albarkacin ranar da kasar Sin ta samu manyan nasarori wajen yin gyare-gyaren harkokin tattalin arziki, gwamnatin kasar Sin za ta kara daukaka ci gaban ayyuka iri daban-daban na raya demokuradiyya,musamman ma a fannin majalisar wakilan jama'ar kasa, da majalisar bada shawara kan harkokin siyasa, da harkokin jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kuma na kananan hukumomi.

Ana sa ran kasar Sin za ta kirkiro irin sabon salon demokuradiyya ,wanda ya fi dacewa da hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin. ( Sani Wang)