Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 16:53:34    
Tsarin taron wakilan jama'ar kasar Sin

cri

Masu karatu, kamar yadda kuka sami labarin cewa, kwanan nan, ana gudanar da taron wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, wanda ya kasance wani kasaitaccen taro a duk fadin kasar Sin. To, taron ya kuma jawo hankulan masu sauraronmu, kuma kwanan baya, bi da bi ne masu sauraronmu suka rubuto mana cewa, suna bukatar karin bayani a game da taron, shin me ya sa aka yi taro, wane ne ke halartar taron, da dai sauransu. To, sabo da haka, yanzu bari in dan bayyana muku tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, don mu fadakar da ku a kan tsarin.

A ranar 5 ga watan nan da muke ciki ne, aka bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadda ta kansace hukumar koli ta kasar Sin, kuma ba shakka wannan al'amari ne mai matukar muhimmanci a cikin harkokin siyasa na kasar Sin.

Madam Hu Xiaoyan wadda ke da shekaru 34 da haihuwa, ta zo ne daga lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, kuma a shekaru 10 da suka wuce, malamar ta je lardin Guangdong da ke gabashin kasar Sin, wanda ke kan gaba wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Bisa kokarinta, yanzu ta zama wani mai kula da dakin sarrafa tangaram na wata ma'aikatar kera tankaram da ke lardin Guangdong. Kwanan nan, a matsayinta na wakiliyar jama'ar kasar Sin daga bangaren manoma, ta yi kokarin tattara ra'ayoyi da shawarwarin da takwarorinta manoma 'yan cin rani suka ba ta. Ta ce, "ina mai da hankali sosai a kan harkar jin dadin manoma 'yan cin rani da batun shigar 'ya 'yansu makaranta. Sabo da jama'a sun zabe ni, shi ya sa ya kamata in dauki nauyin da suka dora mana."

Kamar yadda madam Hu Xiaoyan ta yi, yanzu a nan kasar Sin, akwai mutane miliyan 150 da suka bar gidajensu da ke kauyuka, sa'an nan sun je birane domin cin rani, har ma yawan wadannan manoma 'yan cin rani sun riga sun zarce kashi 1 daga cikin 10 na mutanen kasar Sin. A ranar 5 ga wata, Madam Hu Xiaoyan ta halarci babban taron wakilan jama'ar kasar Sin tare da sauran wakilan jama'a kusan 3000.

Tsarin mulkin kasar Sin ya kayyade cewa, kome ikon kasa, na jama'a ne, kuma taron wakilan jama'ar kasar Sin da kuma tarurrukan wakilan jama'a na wurare daban daban na kasar Sin sun kasance hanyar da jama'a ke bi wajen tafiyar da ikon kasa. Sa'an nan, a kan zabi wakilan jama'a ta hanyar dimokuradiyya, kuma wakilan za su dauki nauyin da jama'a suka dora musu tare kuma da samun sa ido daga wajen jama'a. Wannan shi ne babban tsarin siyasa na kasar Sin, wato tsarin taron wakilan jama'ar kasar Sin.

Daga nan ne muka iya gane cewa, tsarin babban taron wakilan jama'ar kasar Sin tsari ne da jama'a ke kulawa da harkokin kasa. Bisa tsarin, kome ikon kasa, ya kasance a hannun jama'a. To, watakila akwai masu sauraronmu da ke shakkar, Sin kasa ce da ke da dimbin jama'a, shin yaya za a iya tabbatar da ikon tafiyar da harkokin kasarsu ga jama'ar kasar miliyan 1300.

To, bari in muku bayani. Wakilan da aka zaba suna wakiltar jama'a sosai, ciki har da jama'ar da suka zo daga bangarori daban daban a shiyyoyi daban daban da kabilu daban daban da dai sauran fannoni daban daban. Wato ko wane bangare na al'umma na da nasu wakili, kamar yadda madam Hu Xiaoyan ke wakiltar bangaren manoma 'yan cin rani. Domin samun fahimtar tsarin wakilan jama'ar kasar Sin, wakilinmu ya yi hira da mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Mr.Sheng Huaren, kuma ya bayyana mana cewa,

"idan an kwatanta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 da ta 10, za a gane cewa, tsarin wakilan jama'a ya kara kyautatuwa. Wakilan da suka zo daga sassan hukumomin larduna daban daban sun ragu da kashi 1/3, a yayin da wakilan ma'aikata sun karu fiye da ninki daya. Sa'an nan, wakilan manoma sun karu fiye da kashi 70%. Sabbin wakilan jama'a da ke cikin majalisar wakilan jama'a ta 11 an zabe su ne bisa doka kuma ta hanyar dimokuradiyya, sa'an nan, sassan da abin ya shafa sun yi bincike sosai a kansu, sun kuma sami karbuwa sosai daga wajen jama'a."

To, shin yaya wadannan wakilan jama'a ke kulawa da harkokin kasa daban daban a madadin jama'a kuma? To, domin amsa tambayar, yanzu bari in ba ka wani misali. Tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2006, gaba daya ne aka cire kudaden haraji da aka buga a kan aikin noma wanda ke da tsawon tarihi na shekaru 2600 a nan kasar Sin, wanda har aka cire wa manoman kasar Sin nauyin biyan haraji na kudin Sin biliyan 50 a kowace shekara. A hakika dai, da farkon fari, wani wakilin jama'a shi ne ya ba da wannan shawara cikin shirin da ya gabatar. A gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a shekarar 2004, bayan da Mr.Ren Yuqi, wani wakilin jama'ar kasar Sin ya yi bincike sosai a kan kauyukan lardunan Hunan da Guangdong da Fujian da dai sauransu, ya gabatar da wannan babban shirin da ke shawartar a soke kudaden haraji a kan aikin noma. Yayin da wakilinmu ya yi hira da shi, ya ce, "game da shirin da ake gabatarwa, na farko, dole ne a yi bincike sosai, wato manoma nawa ne kuma jama'a nawa ne shirin zai iya bayyana muryarsu. Na biyu, wane irin tasiri ne cire kudaden haraji da ake bugawa kan aikin noma zai iya kawo wa tattalin arziki da zaman al'umma, musamman ma me zai haifar ga jama'a, za mu yi nazari. Na uku, da wuya in kammala wani shiri bisa karfin kaina, shi ya sa muka gayyaci wasu masanan ilmin doka da na noma. Sabo da haka, mun yi kokari sosai wajen fitar da wani shiri."

Shirye-shirye sun kasance matakai da ra'ayoyin da wakilan jama'a suka gabatar wajen daidaita wasu matsaloli. Gabatar da shirye-shirye wani muhimmin aiki ne na wakilan jama'a, haka kuma babban iko ne a gare su.

"jama'a sun zabe ni a matsayin wakilinsu, sa'an nan na zama wakili ne domin jama'a", wannan kalami ne da Mr.Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi yayin da yake bayyana aikin da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 10 ta yi, ya ce, "A cikin shekaru biyar da suka wuce, gaba daya mun kula da shirye shirye 3772 da kuma shawarwari fiye da dubu 29 da wakilai suka gabatar, kuma shirye-shirye da shawarwari da wakilai suka gabatar sun inganta a zahiri, wakilan suna kara taka kyakkyawar rawa."

Wa'adin aikin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kai tsawon shekaru 5, kuma majalisar ta kan kira taronta a kowace shekara. Wato taron shekara shekara da aka bude a ranar 5 ga watan nan da muke ciki ya kasance na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasr Sin. A kan shafe tsawon makonni biyu ana taron.

Yanzu fiye da rabin karni ke nan ana aiwatar da tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kamar yadda shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya ce, tsarin yana ta inganta, "Tsarin wakilan jama'ar kasar Sin ya dace da halin da kasar Sin ke ciki, ya bayyana halin kasar Sin na gurguzu, kuma ya tabbatar da ikon jama'ar kasar wajen kulawa da harkokin kasar Sin. Ya kamata mu tsaya kan bin tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma kyautata shi, ta yadda za a kara inganta tsarin dimokuradiyya da yalwata hanyoyin dimokuradiyya, don jama'a su kara sa hannu cikin harkokin siyasa, su bi hanyoyi daban daban wajen kulawa da harkokin kasa da harkokin tattalin arziki da al'adu da kuma na zaman al'umma."(Lubabatu)