Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 16:41:40    
Duk wani yunkurin yin amfani da batu guda kacal wajen dakushe kwarjinin gasar wasannin Olympics zai ci tura, in ji Liu Guijin

cri
Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Darfur Liu Guijin ya bayyana yau 7 ga wata cewar, yunkurin hada batun Darfur da gasar wasannin Olympics ta Beijing ba shi da tushe, ko shakka babu, duk wani yunkurin yin amfani da batu guda kacal wajen dakushe kwarjinin gasar wasannin Olympics ta Beijing da mutane kalilan suke yi ba zai samu nasara ba.

A wajen taron manema labaru da aka shirya kan batun Darfur a wannan rana a nan birnin Beijing, Mr. Liu ya ce, yunkurin hada gasar wasannin Olympics da wasu batutuwan siyasa wani aika-aika ne bisa tunanin lokacin yakin-cacar-baki.

Liu ya kara da cewar, gwamnatin kasar Sin tana taka rawar a-zo-a-gani wajen daidaita batun Darfur, haka kuma, matukar kokarin da take yi ya samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa. Bangaren Sin ya yi marhabin da duk wata nasiha ko shawara game da gasar wasannin Olympics, kuma yana fatan yin tattaunawa domin samun nagartattun shawarwari. Amma dangane da kowane irin yunkuri na yin amfani da wasu dalilan da ba su da dangantaka da gasar wasannin Olympics ta Beijing wajen kauracewa gasar, da dakushe kwarjinin gasar, ko-ta-yaya bangaren Sin ba zai amince da shi ba.(Murtala)