Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 21:25:23    
Shugabannin kasar Sin sun yi tattaunawa tare da wakilan jama'ar kasar

cri

Ran 6 ga wata, a nan Beijing, daya bayan daya shugaba Hu Jintao da kuma sauran kusoshin kasar Sin sun shiga tarurukan tattaunawa da wasu kungiyoyin wakilai masu halartar tarurukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11 suka shirya.

A lokacin da yake halartar taron tattaunawa da kungiyar wakilan jama'a ta jihar Tibet, ta shirya, shugaba Hu ya bayyana cewa, dole ne a dauki matakan a-zo-a-gani domin ba da tabbaci da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a, da inganta ayyukan kabilu da addinai da kuma yin iyakacin kokari wajen tabbatar da samun jituwa da kwanciyar hankali a zaman al'ummar Tibet.

Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya halarci taron tattaunawa na kungiyar wakilan jama'ar lardin Guizhou. A farkon shekarar bana, Guizhou ta sha wahalar bala'un dusar kankara. Wu ya yi fatan cewa, mutanen kabilu daban daban na Guizhou za su yi iyakancin kokarinsu wajen maido da aikin kawo albarka da sake gina garinsu lami lafiya, za su kuma nemi rage hasara mafi kankanta.

Kazalika kuma, a gun taron tattaunawa da kungiyar wakilan jama'ar lardin Gansu ta kira, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya nuna karfin zuciyar gwamnatin game da kyautata muhallin halittu da kyautata zaman rayuwar masu fama da talauci.(Tasallah)