Saurari
Ana yin cikakken zama na farko na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ta karo na 11 a nan birnin Beijing. A gun taron, za a ba da sharhi kan ayyukan da gwamnatin tsakiya ta yi a cikin shekaru 5 da suka gabata, kuma za a tabbatar da shirin bunkasuwar kasar a nan gaba. Kara sa ido kan tattalin arziki daga dukkan fannoni domin raya tattalin arziki da zaman al'umma a kasar cikin daidaito ya zama ra'ayi daya na wakilan jama'a da hukumomin gwamnatin kasr Sin.
A cikin shekaru 5 da suka gabata, matsakaicin karuwar yawan kudaden samar da kayayyaki, wato GDP ya kai fiye da kashi 10 cikin kashi dari a kowace shekara a nan kasar Sin. Ya zuwa karshen shekarar 2007, jimlar GDP ta kai kudin Sin yuan biliyan 2.4. Sabo da haka, jimlar yawan kudaden tattalin arzikin kasar Sin ta kai matsayi na 4 a duk fadin duniya. A waje daya kuma, jimlar kasafin kudin da gwamnatin tsakiya ta samu ya karu da ninka sau 2, yawan kudin shiga da jama'a suka samu ma ya samu karuwa sosai. Mr. Zuo Wanjun, wani wakilin jama'a, kuma wani manomi daga lardin Sichuan ya ce, "A cikin wadannan shekaru 5 da suka gabata, an soke harajin aikin gona da aka buga kan manoma muhimmin kuduri ne da gwamnatin tsakiya ta tsaida. Sakamakon haka, an sassauta nauyin da ke bisa wuyan manoma. Wannan kuduri ya ba da gudummowa sosai wajen kyautata zaman rayuwar manoma."
Madam Dai Zhaoxia, wata wakiliyar jama'a daga lardin Hunan ta ce, ta cimma burinta na sayen wani babban gida sakamakon karuwar yawan kudin shiga. Ta ce, "gidan da nake kwana yanzu yana da dakuna 3, fadinsa ya kai fiye da murabba'in mita 100. Ya fi tsohon gida kyau sosai. A cikin shekaru 2 da suka wuce, masana'antar da nake aiki ta samu riba sosai, 'yan kwadago ma sun samu moriya a hakika. Yawan kudin shiga da muka samu ya samu karuwa cikin sauri. Sabo da haka, na sayi wani gida a shekarar bara."
Kyautatuwar zaman rayuwar jama'a da wadannan wakilan jama'a biyu suka ji sakamako ne da aka samu bayan da gwamnatin kasar Sin ta canja tunaninta na raya tattalin arziki da zaman al'umma. A da, gwamnatin kasar Sin ta fi mai da hankali wajen saurin cigaban tattalin arziki, amma tun daga shekarar 2003, ta soma canja tunaninta, kuma ta fi mai da hankali wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma cikin halin daidaito. Mr. Liu Shucheng, shugaban hukumar nazarin tattalin arziki ta cibiyar nazarin ilmin zaman al'umma ta kasar Sin ya ce, "dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki shi ne ana son tabbatar da bunkasa tattalin arziki cikin halin daidaito. Kuma an jawo hankulan bangarori daban daban da su canja hanyar neman bunkasuwar tattalin arziki da kyautata ingancin tattalin arziki da tsarin tattalin arziki, amma ba neman saurin cigabansa kawai ba."
Amma kamar yadda firaminista Wen Jiabao ya nuna a cikin rahotonsa da ya gabatar a ran 5 ga wata, ko da yake ana kokarin raya tattalin arziki da zaman al'umma a kasar Sin cikin halin daidaito, amma har yanzu ana samun wasu matsaloli masu tsanani lokacin da ake raya tattalin arziki, kamar su hauhawar farashi kayayyaki da ana zuba jari domin samun kadarori da ba da rancen kudi cikin sauri fiye da kima da dai makamatansu. A gaban wadannan matsaloli, Mr. Ma Kai, shugaban kwamitin neman cigaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki jerin matakai domin fama da wadannan matsaloli. Mr. Ma ya ce, "dole ne a samar da isassun kayayyakin da ake bukata, musamman amfanin gona da kayayyakin masarufi. A waje daya kuma, an kayyade saurin zuba jari da yawan takardun kudi da ake bayarwa."
|