Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 15:55:02    
Kere-keren da jihar Ningxia ke yi wajen bunkasa rawa da tufaffi da kuma kayayyakin ado na kabilar Hui

cri

A matsayinta na wurin da musulmi ke zaune, wanda ya fi girma a kasar Sin, a cikin dogon lokaci, jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta kai ga samun al'adun tuffafi da kayayyakin ado, da kuma fasahar rawa ta musamman.

Tun da 'yan shekarun da suka wuce, bisa abin musamman na al'ummar da ke yankin, jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta dauki matakai, don kiyaye da kuma bunkasa rawar kabilar Hui, da al'adun tufaffi da kayayyakin ado na kabilar. Kazalika kuma, tana ta yin kokari kan yada rawa da tufaffi da kayayyakin ado, ta hanyar yin kere-kere.

Kwanan baya, jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, ta yi nune-nunen tufaffi da wasan rawa ta kabilar Hui a karo na farko a birnin Yinchuan, hedkwatar jihar, inda aka gayyaci kwararru da manazarta na wurare daban daban, wadanda ke kokari kan shirya wasannin rawar kabilar Hui, da kuma nazarin al'adu na tufaffi da kayayyakin ado na kabilar, domin su ba da shawarwari kan kere-kere da bunkasuwar al'adun kabilar Hui. Nasarar da aka samu wajen nune-nunen, ta sanya kwararru daga fanonin rawa, da tuffafi na zamani da su sa idon ganin makoma mai kyau ta rawa da tuffafi da kayayyakin ado na kabilar Hui. Mataimakin shugaban zartaswa na majalisar kwararru a fannin rawa ta kasar Sin Feng Shuangbai ya bayyana cewa, "Wannan nune-nunen da aka yi kan rawa da tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui, ya nuna cewa, fasaha da al'adun kabilar Hui suna kan wani sabon matsayi. Na yi imani cewa, nan gaba za mu kara samun cigaba wajen al'adun kabilar Hui, da fasahar kabilar Hui, musamman ma rawar kabilar Hui, saboda haka, ina sa ido kan wannan."

Nufin shirya wannan nune-nune shi ne, sa kaimi ga ayyukan nazari, da habaka, da kuma yin kere-kere a fannonin rawa, da tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui. Bayan haka kuma, nune-nunen ya gabatar da wata dama mai kyau ga masu ayyukan tsara shirye-shiryen rawa, da zanen tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui, don su yi cudanya, da koyi da juna. Madam Ma Shumin, mai zane-zane daga kungiyar tufaffi da kayayyakin ado ta kananan kabilu ta kasar Sin, tana ganin cewa, "Kwamitin al'umma na jihar Ningxia, da kuma tarayyar al'adu da fasaha ta jihar sun shirya wannan wasan rawa da nune-nunen tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui, a ganina, wannan aiki ne mai hangen nesa, saboda ya kafa wani dandamali ga masu zane-zanen tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui, don su nuna walkiyarsu."

An zabi shirye-shiryen rawa na kabilar Hui guda 57, da kuma tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui 502 a dukkan kasar Sin a gun aikin wasa da nune-nune. Bayan da aka yi zabe sau biyu, a karshe dai, shirye-shiryen rawa 21, da kuma tufaffi da kayayyakin ado 238 na kabilar Hui sun shiga wasa da nune-nunen.

Wadannan shirye-shiryen rawa sun burge joji da 'yan kallon da ke wurin sosai. Wasu daga cikinsu sun nuna imanin addininsu, wasu kuma sun nuna zaman rayuwar 'yan kabilar Hui. Mataimakin shugaban majalisar kwararru a fannin rawa Li Yushan yana ganin cewa, "Shriye-shirye kusan 16 daga cikinsu suna kan babban matsayi a fannonin nuna sabbin ra'ayoyi. Lallai suna bayar mana labarai, kuma suna bayyana abin da ake ji a rai. Wannan abin farin ciki ne ga sha'anin rawa."

Bayan haka kuma, tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui da aka yi nune-nune, su ma sun samu amincewa daga wajen joji. Madam Yu Dan, 'yar majalisar tufaffi ta kasar Sin ta bayyana cewa, "A gani na, dukkan masu zanen tufaffi da kayayyakin ado sun fahimci al'adun kabilar Hui. Kuma sun zane tufaffinsu bisa al'adun kabilar Hui."

Bisa labarin da muka samu an ce, 'yan kabilar Hui da ke zaune a wurare daban daban na kasar Sin, sun kai sama da miliyan 10, saboda haka, ana iya cewa, bunkasuwar kasuwar tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui suna da makoma mai kyau. Hakikanin makasudin da aka shirya wasan rawa da nune-nunen tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Hui shi ne, gabatar da tufaffi na aiki, da na zaman rayuwa na yau da kullum, da dai sauransu, ba kawai suna da kyau ba, har ma sun nuna halin musamman na kabilar Hui.