Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 15:44:50    
Gabar kogin Yangtse dake birnin Wuhan

cri

Jama'a masu sauraronmu assalamu alaikum,barkammu da wannan lokaci,barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na zaman rayuwar Sinawa.Birnin Wuhan,babban birni ne na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin,kogin Yangtse da rassansa suke ratsawa ta birnin nan.Tun farkon wannan karni,gwamnatin birnin Wuhan ta yi kokari wajen kyautata koguna bisa cikakken shirin da ta tsara,ta gina wasu ayyukan hana ambaliyar ruwa da kyautata muhalli daga dukkan fannoni har ta mai da wuraren dake dab da koguna wuraren masu kyau gani.To a cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana.

Ga ciyayi masu tsanwa shur ko ina a wuraren dab da koguna bayan da aka kyautata su a birnin Wuhan.sai ka ce sabon yanki mai tsawo kilomita bakwai dake gabar kogin Yangtse tamkar wani zane mai launin tsanwa ya shimfidu a gefen kogin Yangtse.A yankin nan da akwai filaye iri iri da kayayyakin wasa da na motsa jiki.Wata tsohuwa mai suna Li Yuzheng wadda take da shekaru 82 da haihuwa,tana zama a bakin titin Tianjin na kusa da kogin Yangtse.Ta ga sauye sauyen da aka samu a birnin,da ta waiwayo tarihin yankin,ta gaya wa wakilinmu cewa "Tun shekarun 1970,juji da sauran tarkacen abubuwa da kuma dakunan da aka gina ba bisa doka ba sun mamaye sashen rairayin kogin Yangtse,wadannan abubuwa sun hana ruwan kogin ya gudana yadda ya kamata,har ruwan kogin ya yi sama.da haka kuma matakan da aka dauka domin magance ambaliyarruwa ba su iya taka rawa da suka kamata ba cikin dogon lokaci.Duk lokacin da aka samu ambaliyar ruwa a watan Yuli da na Augusta,mazanan birnin Wuhan su kan yi fama da ambaliyar ruwa."A cikin shekarun baya,gwamnatin birnin Wuhan ta yi iyakacin kokarinta wajen bunkasa birnin cikin sauri,ta zuba kudin Sin RMB Yuan biliyan daya,ta yi shekaru biyar tana inganta ayyukan magance ambaliyar ruwa da kyautata muhalli daga dukkan fannoni.Mr Liu Dongcai,mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta brnin Wuhan ya bayyana cewa

"Domin gina sabon yankin kogin mai kyaun gani da biya bukatun mazaunan,gwamnatin jama'a ta birnin Wuhan ta zabi kwararu daga fannonin magance ambaliyar ruwa da tsare tsare da lambunan shan iska da gine gine da hukumomin tafiyar da harkokin mulkin gwamnatin birnin da kolejojin koyon fasaha ta kafa wata kungiyar tsara fasalin yankin,ta yi koyi da biranen Shanghai da Hangzhou da Suzhou da Hongkong da Seny wajen bunkasa birni.Yayin da take bunkasa birnin ta yi la'akari da launin tsanwa da ruwa da kuma jama'a,ta yi iyakacin kokarinta wajen gina wani sabon yanki mai fadi cike da bishiyoyi da wani yanayi mai dadi."

Mataimakin shugaba Liu Dongcai ya ci gaba da cewa a jikin madatsar ruwan da aka gina tsakanin tashar ruwa ta Wuhan da wurin kwata na Yuehan da akwai kokofi goma,bayan da aka kyautata wurin an rufe kofofi biyar duk domin inganta ayyukan magance ambaliyar ruwa.An kuma kawar da tsohuwar hanyar da aka bi wajen kula da kofofin madatsar,wato a bar ruwan kogin ya gudana ko a datse shi yadda ake bukata a duk lokacin da aka samu ruwan kogin mai yawan gaske.A lokacin da ake samu ruwan sama mai yawan gaske,a bar ruwan sama ya malala kai tsaye zuwa cikin kogin,ta haka aka rage nauyin da madatsar ruwan ya dauka ta yadda za ta kara taka rawa mai amfani wajen magance ambaliyar ruwa.

Lokacin da ake kyautata yankin,gwamnatin jama'a ta birnin Wuhan ta mai da hankali wajen kiyaye halitattu da muhalli.A cikin matakin farko an dauke da kamfanoni da masana'antu 58 daga yankin,haka kuma rushe gine gine masu fadin muraba'in mita dubu dari uku wadanda suka hana ruwan kogin gudu yadda ya kamata,da kwashe jujin daga rairayin kogin da kuma yashe kogin da dasa ciiyayi da furanni,itatuwa masu daraja da kuma kyaun gani da aka dasa sun wuce dubu tamanin,filin da aka dasa ciyayi ya kai fadin muraba'in mita kimanin miliyan daya.Ga shi a yanzu kome ya canza,wata mazauniyar birnin mai suna Wang Jinwen ta gaya wa wakilinmu cewa

"A da mu kan zo nan ne domin kallon kogin,da mun ga ruwan kogin ya yi sama fiye da kima,sai mun ji tsoro kwarai da gaske.Ga shi yanzu muna jin kide kide a gabar kogin da ganin kyakyawan muhali,hankulanmu sun kwanta,lalle muna cikin zaman jin dadi mai faranta rai."

A gabar kogin abin da ya fi daukar idanun mutane shi ne filaye iri iri da aka shimfida a kansa,yawansu ya kai goma sha tara,kowanensu yana da nasa halin musamman inda aka kafa kayayyakin motsa jiki har 450 cikin layi layi,wannan ya samar da sararin shakatawa da nishadi ga mazaunan birnin da masu yawon bude ido.

Ga shi a yau idan ka tsaya kan sabon yankin dab da kogin Yangtse,sai ka manta da ambaliyar ruwa da akan samu a yanayin zafi na kowace shekara wadda ta kan rintsar da birnin nan da kuma kawo barazana ga mazaunan birnin.yanzu mazaunan birnin suna cikin zaman kwanciyar hankali da lafiya ba abun damuwa,suna cikin zaman jin dadi da jituwa.Da yake tofa albarkacin bakinsa kan yankin Kogin,Mr Hu Zilai,wani tsoho mai yawan shekarun sama da sittin ya yi alfahari da cewa

"Wannan yankin ya zama lambun shan iska gare mu ba tare da kashe kudi ba za mu iya zagayawa a nan sau da dama a rana daya.Muna iya yin wake wake da raye raye a nan.Wannan aikin da gwamnatin ta yi ya biya bukatun jama'a,shi ya sa kashi 95 cikin kashi dari na mazaunan birnin nan sun yaba mata."