Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 15:41:41    
Ci gaban labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

----Mai farauta tsuntsaye ya biya kudin diyya. An sami wani mutum a birnin Anyang na lardin Henan na kasar Sin wanda ya jefa duwatsu kan tsuntsaye amma bai yi sa'a ba bai kashe tsuntsa ba ya fashe tagar mota. Sunan mutumin nan Wang aka tilasta masa da ya biya kudin diyya na kudin Sin Yuan dubu daya da dari shida.Malamin nan ya kan kashe tsuntsaye ne da kanana duwatsu duk domin baiwa kyanwa da yake kiwo abinci.Wannan rana da yamma ya jefa kanana duwatsu kan tsuntsaye a hanyar Jiefang a birnin Anyang. Duwatsun da ya jefa ba su sami tsuntsaye ba sun sami tagar wata mota dake gefen hanyar,nan da nan glass din tagar ya fashe.Mai mota ya zo ya kama shi.Ya kirawo dan sanda.Da dan sanda ya zo ya lalashe mafarauta da ya biya kudin diyya ga mai mota na kudin Sin Yuan dubu daya da dari shida.

-----Wani tsoho ya yi karya. Wani tsoho da shekarunsa ya wuce 75 da haihuwa a yankin Xinzhou na birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin ya yi karya ne duk domin samun kudin da zai ba jikokinsu biyu dake fama da rashin lafiya. Sunan tsohon Luo Yinzhang ya ce tun yana da shekaru sama da sittin ya ci gaba da aiki domin samun kudi ga jikokinsa. Iyayen jikokin suna da wani shago na sayar da kayan lambu, duk da haka kudin da suka samu bai isa kudin magani ba sabo da 'ya'yansu na fama da cutar tabarbarewa koda idan ba a warkar da su ba zai zama kanjamo.Daya daga cikinsu biyu na fama da sankarar jini. Kafofin yada labarai na birni Wuhan sun yi kira mazauna birni da su ba da taimakon kudi domin warkar da 'ya'ya biyu.

----Sanya ta shahara domin bikin aure. Sanya wani birni ne dake a kudancin kasar Sin ta shahara sabo da masu yin aure sun je can domin bikin aure ko yawon shakatawa.Tun lokacin da gwamnatin birnin Sanya ta fara shirya bikin auren kungiya a shekara ta 1997,ya zuwa yanzu ta shirya bukukuwan aure domin tagwayen maza da mata dubu biyu. Sanya ta sami suna ne sabo da hasken rana da itatuwan kwakwa da kuma kyakkyawan bakin teku mai rairayi,haka kuma ruwa mai launin shudi ya jawo hankulan masu yin aure.

----An sami wata shirwa mai fuskar biri a lardin Guangdong na kasar Sin. Wani bakauye a gundumar Xuwen ta lardin Guangdong na kasar Sin ya kamo wata shirya mai fuskar biri a ranar talata da ta shige.Batun nan ya jawo hankulan mutane masu yawan gaske. Nauyin shirwa ya kai rabin kilo.Tsawonta ya kai centimeter 25 da digo hudu,an gano ta ne a ciki wani daji na kusa da garin Jinhe.Kwararru sun ce wannan ne karo na farko da aka gano shirwa a wannan bangare,shirwa wani nau'in tsuntsaye da ke karkasin kariyar gwamnatin kasar Sin sun kusan bacewa a doron kasa. An kai shirwa zuwa ga ma'aikatan hukuma masu kula da dazuzzuka,za a yi mata bincike,sannan za a sake ta da ta koma wurin da take so.

----Za ka iya kama dan sane.Wani dan kasuwa mai shekaru 53 da haihuwa a birnin Chongqing dake karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin kai tsaye ya kama yan sane 28 a cikin shekaru goma da suka gabata. Sunan mutumin nan Wei Maohe,yana da kasuwanni guda biyu,daya daga cikinsu na sayar da abin sha ga masu sari, ya fara kama dan sane ne a cibiyar birnin.Daga nan yana sha'awar aikin nan na kama 'yan sane kamar 'yan sanda.Ba wannan aiki yake so kawai ba yana so ya ba da sadaka.Ya kan bayar da taimakon kudi ga wadanda ke fama da talauci. Kwanan baya ya sayar da wani gidansa domin samun kudin taimakawa matalauta.

---'Yan makaranta sun fara rawa maimakon wasannin motsa jiki. Kwanakin baya,'yan makarantar Hutai a birnin Xining na lardin Qinghai sun fara rawa maimakon yin wasannin motsa jiki. Wata rawa ta gargajiya ta 'yan Tibet da ake kira "Guozhuang ta fara bazuwa a tsakanin samari na wannan bangare.. Har ma makarantun firamare da na middle da makarantu masu koyon ilimi mai zurfi sun fara koya 'ya'yansu irin rawa. Wani malamin koyarwa a makarantar firamare ta Beidajie mai suna Ma ya ce abu ne mai kyau ga lafiyar 'yan makaranta,haka kuma 'yan makarantu suna so su yi rawa.