Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 15:29:05    
Har ila yau makomar maido da shawarwarin zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila ba ta tabbatu ba tukuna

cri

A ran 5 ga wata, Madam Condoleezza Rice, sakatariyar harkokin waje ta Amurka ta gama ziyararta a shiyyar Gabas ta tsakiya, lokacin da take magana ga kafofin yada labaru a wannan rana ta ce, shugabannin Isra'ila da na Palesdinu dukkansu sun yarda da maido da shawarwarin shimfida zaman lafiya, yanzu bangarorin 2 suna nan suna hadewa da juna kan yadda za a yi shawarwari a tsakaninsu, amma manazarta sun bayyana cewa, hakikanin abu na gaskiya bai yi daidai kamar yadda Madam Rice ta fada ba.

Da farko, ko da yake Mr. Mahmoud Abbas, shuban hukumar ikon al'ummar Palesdinu ya bayyana nufinsa a wannan rana kan maido da shawarwarin zaman lafiya, ya bayyana cewa, "yunkurin shimfida zaman lafiya wani zaben ne da Palesdinu ta yi kan muhimman tsare-tsare, kuma bangaren Palesdinu yana fatan ci gaba da yin shawarwarin zaman lafiya tsakaninsa da Isra'ila", amma bai bayyana hakikanin lokacin yin shawarwarin ba.

A sa'i daya kuma manazarta sun bayyana cewa, idan Mr. Abbas ya nuna mai da martani sosai kan shawarar da Amurka da Isra'ila suka gabatar, zai jawo illa ga kwarjinin da ya samu daga wajen Palesdinawa. Tun watanni 3 da suka wuce bayan da aka maido da shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palesdinu, kusan an ce ba a samu sakamako ko kadan wajen shawarwarin ba sabo da babban sabanin da ke kasance a tsakanin su.

Na 2, Amurka ta nuna himma kan batun shawarwarin zaman lafiya tsakanin Palesdinnu da Isra'ila, har ila yau kuma gwamnatin Amurka ta tsai da hakikanin makasudin da shugaba Bush zai cimma cikin lokacin aikin sa kan daddale yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Sabo da haka, a gun ziyarar da sakatariyar harkokin waje Rice ta yi, ta dauki alkawari ga Mr. Abbas daga fannoni 2, wato daya shi ne Amurka za ta aike da Mr. David Welch, mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da harkokin shiyyar Gabas ta kusa zuwa kasar Masar don tattauna matsalolin zirin Gaza, an ce wannan ya zama wani muhimmin mataki ne da Amurka ta dauka domin neman tsagaita bude wuta, da sake bude tashoshin kwastan da ke bakin iyakar tsakanin zirin Gaza da kasar Masar. Dayar kuma shi ne, a mako mai zuwa Amurka za ta aike da Mr. William Fraser, jami'in sa ido kan aikin tafiyar da shirin "tasvirar hanyar" shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila zuwa Gabas ta tsakiya don yin shawarwari tare da wadannan bangarorin 2, da duba halin da bangarorin 2 suke ciki wajen tafiyar da shirin.

Kan batun tafiyar da shirin "tasvirar hanyar" shimfida zaman lafiya a Gabas ta tsakiya, tun kafin taron Annapolis da aka yi tsakanin Palesdimu da Isra'ila ma wadannan bangarorin 2 sun riga sun fara tattauna yadda za a gudanar da shirin bisa mataki na farko. Amma bayan da aka maido da shawararin, bangaren Isra'ila ya yi ta yin gine-ginen matsugunan Yahudawa a gabashin birnin Kudus da yammacin gabar kogin Jordan, bangaren Palesdimu kuwa ya gamu da suka daga wajen bangaren Isra'ila sabo da kasa karfin shawo kan halin kwanciyar hankalin da ake ciki a zirin Gaza. Ba za a iya canja irin wannan hali cikin gajeren lokaci ba, kuma wani muhimmin abu shi ne, ko gaskiya ce Amurka tana son tsayawa kan adalci domin daidaita matsalar da ke tsakanin Palesdimu da Isra'ila, sa'an nan kuma ta jawo tasiri sosai gare su.

Yanzu sauran watanni 10 kawai da shugaba Bush na Amurka zai cimma makasudinsa na neman daddale yarjejeniya tun kafin lokacin saukarsa daga karagar mulki, ko za a iya daddale yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Palesdimu da Isra'ila cikin wannan lokaci? Lalle a yi shakka a kan wannan. (Umaru)