Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, an kaddamar da zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 jiya 5 ga wata a nan birnin Beijing. A wajen taron, firaministan gwamnatin kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoton aikin gwamnati, wanda ya jawo hankulan kafofin watsa labarai na ketare da Sinawa 'yan kaka-gida.
Jaridar Tribune de Geneva ta Switzerland ta bayar da labari cewar, gwamnatin kasar Sin tana kara maida hankalinta kan shimfida adalci a zamantakewar al'umma, haka kuma, tana rubanya kokarinta wajen zuba jari cikin aikin ilmantarwa, da jinya, da dai sauran fannonin dake shafar zaman rauywar jama'a.
Wasu kafofin yada labarai na kasashen waje ciki har da Jaridar Washington Post, da Jaridar New York Times ta kasar Amurka sun ruwaito kalaman rahoton aikin gwamnati da firaminista Wen ya yi kan cewar, abin dake gaban kome wajen habaka tattalin arzikin kasar Sin shi ne maida hankali kan inganci, amma ba saurin bunkasuwa ba ne. Kafofin watsa labarai na Amurka su ma sun bayar da labari na cewar Sin za ta zurfafa yiwa gwamnatinta garambawul, kuma a ganinsu, wannan zai taimaka wajen daidaita sassa daban-daban na gwamnatin Sin, ta yadda za a tinkari batun makamashi da kyau, da inganta kiyaye muhalli, da bada taimako ga aikin yin gyare-gyare kan harkokin kudade.
A waje daya kuma, tashar Internet ta Jaridar Ediot Akhronot ta Isra'ila ta ce, a halin yanzu, kasar Sin tana daukar matakai, domin bada cikakken tabbaci cewar, ingancin kayayyakinta ya dace da ma'aunin duniya.
Kazalika, shugaba mai girmamawa ta kungiyar hadin kan 'yan mata Sinawa da na Thailand Liang Bing ta ce, daga wannan rahoto muna iya ganin cewar, gwamnatin kasar Sin tana bada muhimmanci sosai kan batun ilmantarwa.(Murtala)
|