Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 21:33:10    
Kafofin yada labaru na Hong Kong da Macao da kuma Taiwan sun mai da hankulansu kan muhimmin jawabi na Hu Jintao

cri
Ran 4 ga wata, a lokacin da yake ganawa da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin cikin halin aminci, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ba da muhimmin jawabi kan hulda a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan. Daya bayan daya kafofin yada labaru na Hong Kong da Macao da kuma Taiwan na kasar Sin sun dora muhimmanci kan watsa labaru game da wannan muhimmin jawabi, sun kuma ba da sharhi cewa, jawabin zai ba da babban tasiri kan hulda a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan.

Jaridar Wenhui ta Hong Kong ta ba da sharhi cewa, wannan muhimmin jawabin da shugaba Hu ya bayar ya sake shaida aniyar babban yankin Sin da kuma karfin ziciyarta game da kiyaye dinkuwar kasar Sin, ya kuma nuna tunanin babban yankin Sin na neman hada kai da bunkasuwa tare a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan.

A cikin bayanin edita da ta bayar, jaridar Macao Daily tana ganin cewa, jawabin Hu ya nuna illar da aikace-aikacen neman 'yancin kan Taiwan da kuma kawo wa kasar Sin baraka suke kawowa, ya kuma sake nuna sahihanci. Jaridar ta yi imani da cewa, Sinawa 'yan kaka gida da suka hada da al'ummomin Taiwan za su maraba da jawabin.

Sa'an nan kuma, jaridar Lianhe ta Taiwan ta ba da labari cewa, shugaba Hu Jintao ya yi kira ga al'ummomin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan da su hada kansu domin daukaka raya hulda a tsakanin bangarorin 2 cikin lumana.

Kazalika kuma, sauran muhimman kafofin yada labaru na Taiwan sun ba da labaru da yawa game da jawabin da Hu Jintao ya yi.(Tasallah)