Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 21:32:48    
Za a samu babban ci gaba wajen bayar da 'yancin ra'ayi da kuma tsayawa kan bude kofa ga waje da kuma yin gyare-gyare a gida, a cewar Hu Jintao

cri

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi bayani a ran 5 ga wata a birnin Beijing, cewa za a samu babban ci gaba wajen bayar da 'yancin ra'ayi da kuma tsayawa kan bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, da kuma samun sakamako mai kyau wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya da kuma samun jituwar al'umma.

An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar Sin a ran nan a birnin Beijing. A matsayinsa na wani wakilin majalisar, shugaba Hu ya halarci taron kungiyar lardin Jiangsu da yake ciki don tattaunawa kan rahoton aikin gwamnati da firayim minista Wen Jiabao ya yi.

Shugaba Hu ya nuna amincewa sosai ga wannan rahoton aikin gwamnatin kasar Sin. Kuma ya bayyana cewa, ya kamata a kara bayar da 'yancin ra'ayi da kuma sabunta tunani don sa kaimi ga gyare-gayren muhimman fannoni da hanci da kuma daga matsayin bude kofa ga gida da waje, ta yadda za a iya samar da kyakkyawan muhalli a fannin tsari wanda zai taimaka wa samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya.

A ran nan, sauran shugabannin kasar Sin sun tattauna kan rahoton aikin gwamnatin, kuma dukkansu sun nuna amincewa sosai ga rahoton. (Kande Gao)