Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 18:40:35    
Gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta zama gasa ce da za a iya samun 'yan wasan kasar Sin mafi yawa a cikin gasanni masu yawa

cri
A ran 5 ga wata, Cui Dalin, mataimakin shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa, an kiyasta cewa, 'yan wasan kasar Sin kimanin 570 za su shiga manyan gasanni 28 da ke cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing. Sabo da haka gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta zama gasa ce da za a iya samun 'yan wasan kasar Sin mafiya yawa a cikin gasanni masu yawa.

Mr. Cui wani dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, lokacin da yake halartar taron tattaunawa na kungiyar wasannin motsa jiki na taron farko na karo 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, ya bayyana cewa, ban da wasan kwallon tennis da kuma wasan fasahohin doki, ya zuwa yanzu, 'yan wasan kasar Sin 519 sun riga sun samu iznin shiga sauran manyan gasanni 26 da kuma kananan gasanni 214 da ke cikin gasar wasannin Olypics ta Beijing.

Ban da wannan kuma Mr. Cui ya ce, sabo da ba a kammala wasu gasannin samun iznin shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing ba, shi ya sa 'yan wasan kasar Sin za su samu wasu takardun iznin shiga gasar. An kiyasta cewa, yawan 'yan wasan kasar Sin da za su shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing zai kai kimanin 570 gaba daya.(Kande Gao)