Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 20:01:34    
Galibi dai an kammala gina kauyen wasan Olympic na gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
Ran 5 ga wata, a nan Beijing, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, a galibi dai an kammala gina kauyen wasannin Olympic, inda 'yan wasa da malamai masu horar da wasanni da kuma jami'ai masu halartar gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 za su zauna da kuma cin abinci a ciki.

Wannan kauyen wasan Olympic na cikin kusurwa ta arewa maso yammacin wurin yawon shakatawa na wasan Olympic, fadinsa ya kai kadada misalin 66, ya hada da gine-gine 42 da kuma cibiyar ba da hidima. Madam Liu Rong, wakilin mai gina kauyen ta bayyana cewa, yanzu an riga an gama kayatar da gine-ginen a ciki da kuma a waje, haka kuma, an jarraba tsare-tsaren ba da wutar lantarki da samar da ruwa da injunan sanyaya daki. Ban da wannan kuma, an dora muhimmanci kan yin amfani da makamashin da ake iya sake amfani da shi da yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli a lokacin da ake gina wannan kauye.

A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasa da jami'ai fiye da dubu 16 za su zama a kauyen wasan Olympic. Bayan gasar, za a sayar da gidajen da ke kauyen zuwa mazaunen Beijing.(Tasallah)