Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 16:34:27    
Ya kamata a kara shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium yadda ya kamata

cri

Sanin kowa, shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium zai iya shawo kan cutar kashi da ake kiranta "osteoporosis", amma bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka gudanar da bincike, sun gano cewa, sinadarin calcium yana taka muhimmiyar rawa ga jikin mutane a fannoni daban daban, shi ya sa shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium wani abin da ya wajaba ne.

A kwanan nan, kakakin kungiyar kula da abinci ta kasar Amurka kuma kwararriya kan harkokin gina jiki Katharine Talmadge ta bayyana cewa, bincike ya shaida cewa, sinadarin calcium yana iya taimaka wa mutane wajen yin rigakafin sankarar hanji, da sa kaimi ga motsewar tsokar jikin mutane, ciki har da motsewar tsokar zuciya, ta yadda za a iya ba da taimako wajen rage yawan bugun jini da kuma narkar da kitse.

Kuma Madam Talmadge ta ce, Vitamin D wani muhimmin sinadari ne wajen taimaka wa mutane kan karbar sinadarin calcium, amma abinci da yawa ba su kunshe da Vitamin D, shi ya sa ba yadda za a yi, sai matane su rinka samun irin wannan sinadari ta shan hasken rana.

Ban da wannan kuma Madam Talmadge ta nuna cewa, ko da yake yanzu magungunan ba da kariya ga lafiyar jiki da ke kunshe da sinadarin calcium suna nan iri iri, amma dabara mafi kyau ta shan magungunan da ke kunshe da sinadarin calcium ita ce karbar sinadarin ta abinci. Sabo da haka ya kamata mutane su rinka shan isasshiyar madara ko cin abincin da ke kunshe da sinadarin calcium masu yawa a ko wace rana.

Calcium wani muhimmin sinadari ne da ya zama wajibi ga yara lokacin da suke girma. Ko da yake ana iya samun magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium iri iri yanzu, amma fiye da rabin matasa da yawa na kasar Amurka ba su samu isashen calcium da suke bukata a ko wace rana ba. Dalilin da ya sa haka shi ne hanyar zaman rayuwa maras kyau. Kuma a cikin rahoton, an ruwaito kididdigar bincike da ma'aikatar aikin gona ta Amurka ta bayar, cewa a cikin matasa da shekarunsu ya kai 12 zuwa 19 da haihuwa, mata da yawansu ya kai kashi 14 cikin dari da kuma maza da yawansu ya kai kashi 36 cikin dari kawai sun samu isashen sinadarin calcium.

Ban da wannan kuma rahoton yana ganin cewa, hanyoyin zaman rayuwa da suke iya yin illa ga matasan Amurka wajen karbar sinadarin calcium su ne cin kayayyakin kwalama wato fastfood, da shan lemon sosai, da rage kiba da matasa mata su kan yi ido rufe, da yin amfani da na'urar kwamfuta cikin dogon lokaci, da kuma rashin motsa jiki yadda ya kamata da dai sauransu.

Bugu da kari kuma rahoton ya nuna cewa, rashin samun isashen sinadarin calcium zai iya yin illa ga girman matasa. Kuma lokacin da suka tsufa, matasan da ba su samun isashen calcium sun fi saukin kamuwa da cutar kashi da ake kiranta "Osteoporosis", da hauhawar jini, da toshewar hanyoyin jini da kuma cutar sukari.

Sabo da haka hukumar nazari kan kiwon lafiya ta kasar Amurka ta ba da shawarar cewa, ya kamata yara da matasa da shekarunsu ya kai 9 zuwa 18 da haihuwa su karbi sinadarin calcium na miligram 1300 a ko wace rana. Haka kuma hukumar ta nuna cewa, yara da matasa su kan yi girma sosai lokacin da shekarunsu ya kai 9 zuwa 18 da haihuwa. Haka kuma halin lafiyar jiki da suke ciki a wannan lokaci ya kan taka rawa ga lafiyar jikinsu a duk rayuwarsu, shi ya sa suke bukatar karbar isashen sinadarin calcium.