Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 16:30:11    
Wani bikin da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin tashin barcin hunturu

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samuwa da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci, ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.

Bikin tashin barcin hunturu biki ne na uku da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya bayan bikin ruwan sama, wato mai yiyuwa ne bikin ya zo a ranar 5 ko 6 ko 7 ga watan Maris na kowace shekara. Wasu dabbobi suna kan yi barci a duk yanayin hunturu , ana kan cewar barcin din nan barcin hunturu ne. bisa karin bayanin da aka yi a tsakanin jama'a, an bayyana cewa, bayan bikin tashin barcin hunturu, yanayin sararin samaniya ya kara samun dumi, kuma ana soma cida a karo na farko a yanayin bazara, cidar din ta yi wa dabbobin da ke barcin hunturu fargaba, saboda haka dabbobin suna soma fita waje suna abinsu. An kuma soma kyankyasa wasu kwayayen tsutsotsi da ke karkashin kasa. Saboda haka, bikin tashin barcin hunturu shi ne wani bikin yanayin sararin samaniya da ya bayyana halin da halittu da yanayi suke ciki . A gaskiya dai, tashin barcin hunturu da dabbobi suka yi ne ba bisa sanadiyar jin muryar aradu ba, amma bayan yanayin sararin samaniya ya kara dumi, kuma bayan zafin kasa ya kara yin sama, sai dabbobi su soma fita waje don yin abinsu .

Tun daga zamani aru aru na kasar Sin , mutanen kasar Sin sun mai muhimmanci sosai ga bikin, a ganinsu, bikin ya zama ranar soma aikin gona a yanayin bazara. Karin magana ya bayyana cewa, bayan ranar bikin tashin barcin hunturu, bai kamata ba a yi hutu wajen aikin noma . Duk saboda aradun yanayin bazara ya yi cida , kuma tsire-tsiren halittu suna girma da kyau, ana kuma kara zafi tare da samun ruwan sama da yawa. Ya kamata a yi aikin maimai a gonaki .

A tsakanin jama'ar kasar Sin, ana kan cewa, idan ana ta jin cidar aradu a karo na farko kafin ranar bikin tashin barcin hunturu, to za a sami ruwan sama da yawa a wannan shekara, idan ana ta jin cidar aradu a daidai ranar bikin tashin barcin hunturu, to tabbas ne za a sami kaka mai armashi ko da aka noma wadanne ne shuke-shuke . Amma idan ranakun da yawa da suka wuce ranar bikin tashin barcin hunturu, ba a ji cidar aradu ba, to za a yi karancin ruwan sama a shekarar, kuma ba za a sami kaka mai armashi ba.

A ranar bikin tashin barcin hunturu, a lardin Kwangdong da ke kudancin kasar Sin, mutane suna da al'adar yin bikin sallar layya, wato wasu suna yin bikin nuna girmamawa ga damisa mai farin gashi. Ana jita jita cewa, damisa mai farin gashi yana daya daga cikin mugayen dodanni, a ranar, za ta fita waje don neman abinci. A zamanin da, ana noma sosai, damisoshi suna kawo barna mai tsanani sosai a kan aikin noma da rayukkan mutane. A wannan rana, mutane sun yi bikin nuna girmamawa ga damisa duk domin neman samun zaman lafiya ne, a cikin sinawa masu asalin lardin Kwangdong da ke zama a kasashen waje , sun iya shirya wasu aikace-aikace na yi wa mutane marasa halin kirki duka, wato a wannan rana, mutane sun tafi zuwa haikalin ibada don yi wa hotunan mutane marasa halin kirki duka ta hanyar yin amfani da takalma, a ganinsu, ranar bikin tashin barcin hunturu ta taso, ba ma kawai mugayen tsutsotsi dukansu sun fita waje ba, hatta ma wadanda suke da halin marasa kyau su ma suna fita waje, shi ya sa, bayan da aka yi wa wadandan mutane duka, to za a iya zaman rayuwa lami lafiya a duk shekarar, kuma mutane suna cikin zaman jituwa sosai. Wadannan ayyukan da aka yi sun bayyana buri mai kyau da zaman alheri da mutanen kasar Sin suke son samuwa.(Halima)