Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 15:52:24    
Kasar Iran na ja-in-ja tare da kasashen yammaci a kan sabon kudurin kwamitin sulhu

cri

Jiya ranar Talata, Mohammad Ali Hosseini, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya bayar da sanarwa cewa, kudurin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartas a karo na uku don kakaba wa kasar Iran takunkumi ba shi da amfani, haka kuma ya ce, kasarsa za ta ci gaba da gudanar da shirin nukiliyarta. A ganin manazarta, wannan ya nuna cewa, kasar Iran ta riga ta fara ja-in-ja a tsakaninta da kasashen yammaci wadanda Amurka ke shugabanta a kan sabon kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

A cikin sanarwar da ya bayar a wannan rana, Hosseini ya bayyana cewa, "wannan kuduri ya saba wa manufofi da tsarin dokoki na hukumar makamashin nukiliyar duniya, an zartas da shi ne domin manufar siyasa, sabo da haka ba shi da daraja, kuma ya kamata, a yi Allah wadai da shi. Ya kara da cewa, kudurin ba zai kawo tasiri ko kiris ga aniyar da jama'ar kasar Iran da gwamnatinta suka dau don gudanar da shirin raya nukiliya bisa halalen ikonsu ba.

Ali Larijani, tsohon babban wakilin kasar Iran mai kula da shawarwarin nukiliya shi ma ya bayyana a wannan rana cewa, za a yi babban zaben 'yan majalisar dokokin kasar Iran nan gaba kadan, a tashoshin jera kuri'a, jama'ar Iran za su mayar da martani ga wannan kudurin kwamitin sulhu.

Jiya, Mahmoud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya yi kashedi cewa, dukkan sabon takunkumin da za a kakaba wa kasar Iran, zai kawar da kwarjinin kwamitin sulhu kwata-kwata. Ya kuma kara da cewa, kwamitin sulhu ya tsaida tsoffin kuduransa a kan shirin nukiliyar kasar Iran bisa labarun kuskure, haka kuma ya sake yin kuskure wajen tsai da sabon kuduri a shekaran jiya. Wannan zai dakushe kwarjinin kwamitin sulhu.

A wannan rana, Ali Asghar Soltanieh, zaunannen wakilin kasar Iran a hukumar makamashin nukiliyar duniya ya bayyana cewa, babu wani abun da sabon kudurin zai yi ba, sai ya dakushe karfin da hukumar makamashin nukiliyar duniya ke da shi wajen daidaita batutuwa, da kuma tauye kokarin da ta yi a da. Alaeddin Boroujerdi, shugaban kwamitin kula da tsaron kasa da huldar waje na majalisar dokokin kasar Iran shi ma ya ce, mai yiwuwa ne, sabon kudurin da aka zartas don kakaba wa kasar Iran takunkumi, zai kawo mugun tasiri ga sharwarwarin da ake yi a tsakanin Iran da kungiyar tarayyar Turai.

Shekaran jiya, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya amince da sabon kudurin da kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka gabatar don kakaba wa kasar Iran takunkumi. A karkashin sabon kudurin, za a haramta wa jami'an kasar Iran ziyara a kasashen yammaci, da kara kakaba wa kasar Iran takunkumi a fannin tattalin arziki da cinikayya da kudi, da bai wa kasashe daban daban ikon daukar matakai wajen binciken kayayyakin kasar Iran da sauransu. Haka kuma kudurin ya jaddada cewa, ya kamata, a kara inganta kwarjinin hukumar makamshin nukiliyar duniya, an amince da ci gaban da aka samu wajen yin hadin gwiwa a tsakanin hukumar da kasar Iran, an nuna goyon baya ga ci gaba da yin hadin gwiwarsu.

Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, bayan da kwamitin sulhu ya amince da kuduri na uku a kan kakawa wa kasar Iran takunkumi, kasar Iran ta yi kokari sosai wajen yin ma'amala da hukumar makamashin nukiliyar duniya, sa'an ta yi amfani da damar da ta samu wajen yin shawarwari a tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai, don kauce wa sabon takunkumin da za a kakaba mata, har da hadarin daukar matakin soja a kanta. Daga wannan, aka iya gano cewa, yanzu, an riga an sake fara ja-in-ja a kan batun nukiliyar kasar Iran. (Halilu)