Ran 5 ga wata, a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, a sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta dage kan manufar siyasa ta mulkin kanta da zaman lafiya, da nacewa ga bin hanyar bunkasuwa cikin lumana, da manyan tsare-tsare na bude kofa ga kasashen waje bisa moriyar juna da cimma nasara tare, da ciyar da gina dauwamammen zaman lafiya da bunkasuwa tare cikin duniya mai jituwa.
Wen Jiabao ya bayyana haka ne yayin da ya bayar da rahoton aiki na gwamnati a gun taron shekara-shekara na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a wannan ranar, Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata mu yi kokarin samar da bunkasuwar hulda tare da kasashe masu sukuni, mu zurfafa dangantakar makwabtaka ta aminci tare da kasashen da ke makwabtaka da mu daga dukkan fannoni, kuma mu kara karfimmu wajen inganta hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa, mu yi kokarin kaddamar da manufar siyasa tare da bangarori daban-daban, da ciyar da aikin warware manyan batutuwa masu zafi da batutuwan duniya, don kiyaye halalen hakkin na jama'ar Sin da hakkin mutanen kasar Sin a ketare. (Bako)
|