Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 12:01:06    
Yawan masu aikin sa kai na wasannin Olympic da wasannin Olympic na musamman na Beijing ya wuce miliyan guda

cri
Yawan masu aikin sa kai da suka yi rajistar sunayensu domin neman shiga ayyukan ba da taimako ga wasan Olympic da wasan Olympic na musamman na Beijing yana ta kara karuwa, ya zuwa ran 4 ga wata, yawan masu aikin sa kai na wasanni ya riga ya wuce miliyan guda, yawan masu aikin sa kai na ba da hidimomi a birane kuma ya kai miliyan guda da dubu 200.

Tun daga shekarar 2006, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fara aikin nema daukar aikin sa kai daga dukan mutanen kasar Sin, da 'yan uwanmu na Hong Kong da Macao da Taiwan da Sinawa 'yan kaka gida da kuma mutanen kasashen waje bi da bi. Yanzu, sabo da wasannin Olympic yana karatowa, mutane na bangarori daban daban na kasar Sin sun kara nuna kwazo da himma wajen neman damar ba da hidima ga wasannin Olympic na Beijing.

Bisa labari da aka samu, an ce, a lokacin wasannin Olympic da wasannin Olympic na musamman na Beijing, za a bukaci masu aikin sa kai na ba da hidimomi a wasanni dubu 100, kuma masu aikin sa kai na ba da hidimomi ga birane dubu 400. (Zubairu)