Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 10:59:26    
Jaridar People's Daily ta bayar da bayanin edita don taya murnar kaddamar da zama na farko na majalisar dokokin kasar Sin a karo na 11

cri
Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, da safiyar yau 5 ga wata din nan ne, aka kaddamar da zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 a nan birnin Beijing. Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da wani bayanin edita mai lakabi haka "Tafiyar da ayyuka daidai bisa fatan al'umma, daukar babban nauyin da jama'a suka danka", don taya murnar kaddamar da taron da hannu bibbiyu.

Bayanin ya ce, wakilan majalisar dokokin kasar Sin kusan 3000 daga wurare daban-daban, da sana'o'i daban-daban, sun tattauna kan manyan harkokin kasar Sin, da harkar bunkasuwa, da gudanar da shawarwari, da aiwatar da ikon kasa. Wannan dai ya kasance wani babban al'amari a zaman siyasa na kabilu daban-daban na kasar Sin.

Bayanin ya kara da cewar, babu shakka, kaddamar da wannan babban taro zai haifar da muhimmin tasiri ga daukaka cigaban sha'anin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin. Ya kuma yi imani cewar, wakilan jama'a daban-daban za su tafiyar da ayyukansu daidai bisa fatan al'umma, su dauki babban nauyin da jama'a suka danka musu, domin kammala dukkanin harkokin taron da aka tanada cikin nasara, da sauke muhimmin nauyin dake bisa wuyansu a wannan zamani.(Murtala)