Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 09:30:05    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (27/02-04/03)

cri

A ran 27 ga watan jiya, agogon wurin, kwamitin wasannin Olympic na kasar Greece ya yi taro, inda aka tsai da kuduri cewa, 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Maria Nafpliotou za ta zama mai karbar wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing ta shekarar 2008. Bisa shirin da aka tsara, a ran 24 ga wata, mai karbar wutar yula za ta karbi wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing a tsohon wurin Olympia.

A ran 24 ga wata, za a yi bikin karbar wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing a birnin Olympia na kasar Greece, wannan ya alamanta cewa, daga wannan rana, za a fara aikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing a hukunce. Kirarin aikin shi ne "Kunna kuzari, kuma mika mafarki". Za a gudanar da aikin a kasashen waje daga ran 1 ga watan Afrilu zuwa ran 3 ga watan Mayu, a cikin gida na kasar Sin kuwa, za a mika wuta yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing daga ran 4 ga watan Mayu zuwa ran 8 ga watan Agusta.

Ran 2 ga wata da dare, aka rufe zama na 49 na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur tsakanin kungiya kungiya a birnin Guangzhou na kasar Sin. A gun zagaye na karshe na gasa tsakanin kungiyoyin maza a wannan rana da dare, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Korea ta kudu ta samu zama ta farko a kungiyar maza, wannan karo na 16 ne da ta zama zakaran kungiyar maza ta gasar cin kofin duniya. Kungiyar kasar Korea ta kudu ta samu zama ta biyu, kungiyar Hongkong ta kasar Sin da kungiyar kasar Japan sun samu zama na uku tare. A gun zagaye na karshe na gasar dake tsakanin kungiyoyin mata a ran 1 ga wata, kungiyar mata ta kasar Sin ta lashe kungiyar mata ta kasar Singapore ta zama zakara. An bude wannan gasa ne a ran 23 ga watan jiya, gaba daya kungiyoyi 72 da suka zo daga kasashe da shiyoyyi fiye da 130 sun halarci gasar. Za a yi zama na 49 na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur tsakanin mutum daya daya a birnin Yokohama na kasar Japan a shekarar 2009.

Ran 29 ga watan jiya, a gun gasar sada zumunta ta wasan kwallon kafa ta mata da aka shirya a birnin Freiburg na kasar Jamus, kungiyar kasar Jamus wadda ita ce zakarar duniya ta lashe kungiyar kasar Sin da ci 2:0, wannan shi ne gasa ta 23 dake tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin da ta kasar Jamus. (Jamila Zhou)