Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 21:30:13    
Mr. Wen Jiabao ya bukaci a yi kokari domin samun saurin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata

cri

Ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya nuna cewa, dole ne a raya tattalin arzikin daga manya fannoni da sauri, da karfi, kuma kan muhimman abubuwa yadda ya kamata, domin samun saurin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.

Mr. Wen Jiabao ya nuna haka yayin da yake gai da membobi masu halartar zama na farko na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa a karo na 11 da kuma yin shawarwari tare da su. Ya ce, bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru 30 da suka wuce tun da aka fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta sami cigaba sosai wajen samar da kayayyaki da fanin fasaha, tana da dama da yawa wajen fadada kasuwanni a gida, da daidaita tsarin tattalin arziki, da kirkira sabbin fasahohi da kanmu, da kyautattan zaman al'umma, kuma akwai kasancewar damar raya tattalin arziki. Dukkansu su ne kyakkyawan sharudda wajen aiwatar da aikin raya tattalin arziki a shekarar da muke ciki.