Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 21:18:39    
Dole ne a nemi tabbatar da zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan, in ji shugaba Hu Jintao

cri
Ran 4 ga wata, a nan Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa, tilas ne a a raya dangantaka a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, kuma a nemi kawo wa 'yan uwanmu na bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan alheri da kuma tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki cikin sahihanci, haka kuma, a kiyaye ikon mulkin kan kasa da cikakken yankunan kasa da kuma babbar moriyar al'ummar kasar Sin.

Shugaba Hu ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da mambobin kwamitin duk kasa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11, wadanda suke halartar taro na farko na majalisar, kuma su ne mambobin kwamitin juya juyin hali na jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da kuma wasu al'ummomin Taiwan.

A gun ganawar, Hu ya ce, babban yankin Sin yana son yin tattaunawa da shawarwari tare da dukkan jam'iyyu a Taiwan, wadanda suka amince da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Za su yi shawarwari cikin adalci kan batutuwa da yawa, za su tattauna kan dukkan batutuwa.

Ya kuma kara da cewa, aikace-aikacen neman 'yancin kan Taiwan da kawo wa kasar Sin baraka sun keta tunanin al'ummar kasar Sin na kiyaye dinkuwar kasa, za su ci tura, tabbas ne ba za su sami nasara ba. Ko kusa kasar Sin ba ta yi sassauci kan neman 'yancin kan Taiwan da kawo wa kasar Sin baraka ba.(Tasallah)