Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 16:43:35    
Kasar Sin za ta cigaba da bin manufar bude kofa ga kasashen waje

cri

Kakakin taron farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta karo na 11 Jiang Enzhu ya bayyana a ran 4 a nan birnin Beijing cewa, muhimmin kashi na bude kofa ga kasashen waje da kasar take yi shi ne jawo jarin kasashen waje zuwa kasar Sin, shi ya sa, kasar Sin za ta cigaba da bin manufar bude kofa ga kasashen waje ba tare da kasala ba, kuma ta yi maraba da 'yan kasuwa na kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin.

Yayin da yake ganawa da manema labaru, Jing Enzhu ya ce, tun daga shekarar bara har zuwa yanzu, kasar Sin ta aiwatar da jerin gyare-gyare kan manufar dake da nasaba da aikin zuba jari na 'yan kasuwan kasashen waje, mai yiwuwa ne, wadannan shari'u da ka'idoji da matakan gyare-gyare da kasar Sin ta tsara za su kawo tasiri ga kamfannonin kasashen waje dake kasar Sin, amma an tsara wadannan manufofi ne domin kafa wata halattacciyar kasuwa mai adalci kuma a fili ga kamfannoni daban daban, ta yadda kamfannonin za su dace da sabon halin da kasar Sin ke ciki wajen bunkasa tattalin arziki don samun bunkasuwa. Idan aka yi hangen nesa, wadannan manufofi za su iya kawo moriya ga kamfannonin kasashen waje don kara karfin takararsu da samun bunkasuwa yadda ya kamata.(Lami)