Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 16:16:41    
Yufo, Gidan ibada na addinin Buddha

cri

Gidan ibada na addinin Buddha na Yufo da ke birnin Shanghai aka gina shi a sheakar 1882. Ma'anar Yufo a Sinance ita ce mutum-mutumin Buddha da aka yi da lu'ulu'u irin na jade. Bayan da aka yi juyin mulki a shekarar 1911, an kyale shi, ba a kula da shi yadda ya kamata ba, shi ya sa a tsakanin shekarar 1918 zuwa shekarar 1928 an sake gina shi a wurin da muka gani a yau.

Mutum-mutumin Buddha 2 na lu'ulu'u da ke cikin wannan gidan ibada su ne wasu 2 daga cikin dukkan mutum-mutumin Buddha guda 5 na lu'ulu'u da dan addinin Buddha Huigen na babban tsaunin Putuo ya kawo daga kasar Burma wato kasar Myanmar ta yanzu a shekarar 1882. An taba ajiye su a bayan gari na birnin Shanghai a farko. Gidan ibada na Yufo ya hada da manyan zaunuka guda 3, wato babban zauren na Maitreya, da babban zauren Daxiongbaodian da kuma babban zauren Sanshengdian. A cikin babban zauren Maitreya, an ajiye mutum-mutumin Buddha mai suna Maitreya wato Buddha da ke kan murmushi. A cikin babban zauren Daxiongbaodian, wato babban bangare na gidan ibada na Yufo, an ajiye mutum-mutumin Sakyamuni tare da mabiyansa 2 a dab da shi, wadanda ya fi so, wato Ananda da kuma Kasyapa.

A cikin babban zauren Yufo, akwai wani mutum-mutumi mai tsayin misalin mita 1.9 na Sakyamuni da aka kera da lu'ulu'un jade. Sakyamuni, wanda ya kafa addinin Buddha, ya zauna a nan cikin lumana. Sa'an nan kuma, in masu yawon shakatawa sun kawo ziyara a babban zauren Wofo, suna iya ganin wani kwantaccen mutum-mutumin Sakyamuni, wanda aka kera da lu'ulu'un jade mai launin fari, tsawonsa ya kai misalin santimita 96. Ma'anar Wofo a Sinance ita ce Buddha da ke kwanta.

Dadin dadawa kuma, an nuna kyawawan mutum-mutumi masu daraja da aka yi a zamanin daular Beiwei da na Tang na kasar Sin wato a tsakanin shekarar 386 zuwa ta 534 da kuma a tsakanin shekarar 618 zuwa ta 907 a cikin dakin nune-nune a gidan ibada na Yufo. Baya ga wadannan mutum-mutumi kuma, an ajiye littattafan addinin Buddha da zane-zane da aka waiwaya da hannu a zamanin daular Tang na kasar Sin.

'Yan addinin Buddha fiye da 70 su kan yi ayyukan yau da kullum a gidan ibada na Yufo. Ban da wannan kuma, in masu yawon shakatawa sun ji yunwa a lokacin da suke ziyara a gidan ibada na Yufo, to, wani dakin cin abinci da wannan gidan ibada ke tafiyar da shi yana iya samar da ire iren abinci masu dadin ci. Wannan dakin cin abinci ya ji alfahari sosai saboda yana samar da dukkan abinci da kayayyakin lambu da Tofu, ko da yake sunayen wadannan abinci suna shafar nama da kifi da nama kaji da naman agwagi.