Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 20:03:31    
Tsohon babban magatakardar MDD ya bar Kenya, bayan an samu cimma yarjejeniyar siyasa a kasar.

cri

Ranar lahadi ne tsohon babban sakataren MDD, kuma babban mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar Kenya, Mr. Kofi Annan, ya bar kasar Kenya, bayan da ya samu nasarar sasanta rikicin siyasar kasar wanda yayi kamari, abinda ya bayar da wata kafa ta cimma yarjejeniyar raba mukaman siyasa tsakanin shugaba Mwai Kibaki da jagoran 'yan adawa na kasar,Mr. Raila Odinga.

A cikin jawabinsa, Mr. Kofi Annan yace yanzu zai mika aikin shiga tsakanin ga hannun ministan kula da harkokin waje na Nijeriya, Mr. Oluyemi Adeniji, yayin da shi kuma zai nufi Uganda, daga bisani kuma ya wuce Geneva domin gudanar da wasu ayyukan.

Tsohon babban magatakardar na MDD, yace yaji dadin wannan aiki na shiga tsakani, domin kuwa baya ga damar da ya samu ta sanin shugabannin kasar, ya kuma samu wata dama ta sanin membobin kungiyoyi masu zaman kansu da jama'a da dama na kasar.

A ranar Asabar ne Mr. Annan ya gana da jami'an diplomasiyya na Afirka da Turai, da shugabannin addini, domin tattaunawa kan yarjejeniyar da aka cimmawa ranar Alhamis, wadda zata kawo karshen tashin hankalin da ya barke a kasar ta Kenya bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa.

Yanzu dai wakilan gwamnati da na 'yan adawa suna maida hankali kan mahimman batutuwa na dogon lokaci, da suka hada da batun rarrraba filaye, dangantaka tsakanin kabilu daban daban na kasar, da kuma yiwa kundin tsarin mulkin kasar garambawul. A makon gobe ne ake sa ran za a ci gaba da tattaunawar.

Zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Decemban bara ne ya haddasa barkewar tashin hankali a kasar ta Kenya, abinda yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu daya, yayin da sama da mutane dubu dari shidda suka rasa gidajensu.

Ranar Litinin ce ake sake komawa kan teburin shawarwari tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa, bayan an kwashe sama da wata guda ana ta kai ruwa rana a wajen tattaunawar ba tare da samun ci gaba ba.

Mr. Annan yace yayi farin ciki bisa ga yadda tattaunawar ta gudana a ranar Juma'a, inda aka tabo batutuwan zabe, da yin kwaskwarima ga ikon mallakar filaye da kuma batun talauci da yayiwa jama'a katutu.

Yace a bayyane yake cewa dukkan bangarorin biyu sun himmatu kan wadannan batutuwa, kuma yayi amannar cewa tattaunawar zata gudana ba tare da tangarda ba.

Kofi Annan yace ko da ya bar kasar ta Kenya, to ba zai yi nisa, kuma duk lokacin da aka bukace shi zai sake komawa kasar cikin dan kankanen lokaci, sannan kuma lokaci lokaci zai rinka tuntuba domin jin inda aka kwana dangane da tattaunawar. Sabo da haka a halin yanzu aikin shiga tsakani da sasantawa tsakanin bangarorin biyu a kasar Kenya, zai kasance a hannun Mr. Oluyemi Adeniji, ministan harkoikin waje na Nijeriya,

Ranar Alhamis ne shugaban Mwai Kibaki da Raila Odinga, jagoran 'yan adawa suka rattafa hannu a kan wata yarjejeniya ta kafa gwamnatin hadin guiwa, da nufin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Kafin Mr. Annan ya bar kasar a Kenya, saida ya gana da jagoran 'yan adawa. Mr. Odinga da shugabannin 'yan kasuwa na kasar a ranar asabar, inda aka tattauna kan irin rawar da zasu taka wajen sake gina kasa.

Mr. Odinga yayi nuni da cewa samun nasarar yarjejeniyar rarraba mukaman siyasa ta dogara kan mahimman bangarorin biyu. Yace shugaba Kibaki ya bamu tabbaci, kazalika ni ma na bayar da tabbaci ga tawagar shiga tsakanin, cewa zamu bayar da cikakken goyon baya ga wannan shirin doka, ta yadda za'a gabatar da ita ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma kara jaddada aniyarsa, ta ganin an samu nasara kan wannan yarjejeniya, ya kuma bayyana cewa zai gana da shugaba Kibaki domin tsara hanyoyin da za'a bi domin samun ci gaba.

Shima kakakin majalisar dokokin kasar ta Kenya, Mr. Kenneth Marende ya fadi ranar juma'a cewa, baya tsammanin za'a samu wata matsala wajen gabatar da wannan shirin doka ta yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai bayar da ikon rarraba mukaman siyasa.

A karkashin yarjejeniyar, Shugaban Mwai Kibaki shine zai shugabanci gwamnatin hadin guiwar, yayin da ake sa ran Mr.Odinga ya zama Priministan kasar, kuma ma'aikatun gwamnatin kasar zasu kasance karkashin ikon sa. [Lawal]